Musulmai Na Ci Gaba Da Nuna Fushinsu Kan Mawakin Kudu Davido
- Mawaƙin Kudancin Najeriya Davido na ci gaba da shan suka kan bidiyon wata waƙa da ya sanya a shafinsa na Twitter
- Musulmai da dama sun yi ta suka da caccakar mawaƙin kan bidiyon da ya sanya wanda ya taɓa ƙimar addinin musulunci
- Wani matashi ya bi sahu wajen raba gari da mawaƙin inda ya yayyaga duk wasu hotuna na tallar waya ɗauke da mawaƙin a jikinsu
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Bidiyon waƙar da mawaƙin Kudancin Najeriya ya sanya a shafinsa na Twitter ya fusata ran musulmai sosai a faɗin ƙasar nan, inda suka nuna ɓacin ransu kan rashin mutunta musulunci da mawaƙin ya yi.
A cikin bidiyon na ɗaya daga cikin mawaƙan dake a ƙarƙashin Davido, an nuna wasu mutane a masallaci suna yin Sallah, inda bayan sun kammala kuma suka koma suna tiƙar rawa.
Rashin Biyan Kudin Shagulgula Ya Sanya Amarya Ta Soke Aurenta Ana Saura Sati 1 Biki, Iyaye Sun Ba Ta Muhimmiyar Shawara
Hakan ya sanya musulmai sun yi ca akan mawaƙin domin nuna rashin dacewar wannan bidiyon wanda ya taɓa ƙimar addinin musulunci.
Nan da nan aka yi ta suka da caccakar mawaƙin domin yin Allah wadai da wannan bidiyon da ya ɗora wanda ya ci zarafin addinin musulunci.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Mutane da dama da suka yi arba da bidiyon sun ɗauki matakin daina sauraron waƙoƙin mawaƙin, daina bibiyarsa a shafukan sada zumunta tare da yin kira ga sauran musulmai da su bi sahu wajen yin hakan.
Matashi ya yayyaga hotunan Davido
Wani matashi mai sana'ar siyar da wayoyi wanda ya sanya hotunan tallar da mawaƙin yake yi wa kamfanin waya na Infinix, ya bi dukkanin hotunan mawaƙin dake a shagonsa ya yayyaga su.
A cikin wani bidiyo da wani mai amfani da sunan @Smaga406 a Twitter, an nuna matashin yana yage dukkanin hotunan tallar wayar da mawaƙin yake yi daga cikin shagonsa da yake yin sana'a.
Da Dumi-Dumi: 'Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Farmaki Gidan Tsohon Minista a Najeriya, Sun Tafka Barna
Mutane da dama sun yaba masa kan yadda ya raba jiha da wanda ya nuna rashin girmamawa ga addinin musulunci.
Davido Ya Ji Wuta Ya Goge Bidiyon Da Ake Cece-Kuce
A wani labarin kuma, mawaƙi Davido ya goge bidiyon da ya janyo cece-kuce wanda ake cin mutuncin Sallah a cikinsa.
Mawaƙin dai ya goge bidiyon ne bayan ya sha suka da caccaka daga wajen musulmai waɗanda suka yi tir da yaɗa bidiyon da ya yi a shafinsa na Twitter.
Asali: Legit.ng