'Yan Sandan Nasarawa Sun Damko Mutane 2 a Jihar Taraba Bisa Zargin Satar Mota
- 'Yan sandan jihar Nasarawa sun sanar da kamo wasu mutane su biyu bisa zargin satar wata mota a lafiya babban birni jihar
- 'Yan sandan sun ce sun yi nasarar kamo barayin ne daban-daban a Gembu jihar Taraba, da kuma jihar Filato
- Barayin da aka kama sun amsa laifin da ake zarginsu da shi, inda suka bayyana cewa sun hada baki wajen sayar da motar kan naira miliyan 2.5
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Lafia, Jihar Nasarawa - Rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa ta cafke wasu mutane biyu da ake zargi da satar mota a karamar hukumar Lafia da ke jihar.
Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandan jihar, DSP Ramhan Nansel, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Lafia babban birnin jihar ranar Lahadi kamar yadda The Punch ta wallafa.
Sun gudu zuwa Taraba da Filato bayan sace motar
Nansel ya bayyana cewa, bayan sace motar, wadanda ake zargin masu shekaru 49 da 38, sun tsere zuwa jihohin Taraba da Filato, sai dai an kama su bayan jajircewa da jami’an ‘yan sandan suka yi wajen tsananta bincike.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Nansel ya kara da cewa, a ranar 19 ga Yuli, 2023, da misalin karfe 4 na yamma ne aka kawo musu batun satar motar, wacce Toyota Corolla kirar 2015 ce.
Masu korafin sun ce sun bai wani makanike gyaran motar ne,inda wadanda ake zargi suka yi awon gaba da ita.
Nansel ya ce sakamakon korafin da aka shigar, jami’an ‘yan sanda da ke aiki a wani sashen na jami'an 'yan sandan Lafia suka tsunduma cikin bincike mai zurfi kan lamarin.
Ya bayyana cewa a cikin hakan ne suka yi nasarar kama Sani Labaran a garin Gembu da ke jihar Taraba. Sani mai kimanin shekaru 49, ya ce shi dan asalin Titin Shinge da ke Lafia ne.
Matasa Sun Kutsa Katafaren Rumbun Ajiyar Kayayyaki Na Ɗan Majalisa, Sun Tafka Ta'adi, An Rasa Rayuka a Arewa
Barayin sun hada baki domin sayar da motar kan naira miliyan 2.5
Jami'an sun kuma yi nasarar kama abokin aikin nasa, Ibeto Nwobodo, dan garin Faringada da ke jihar Filato, mai kimanin shekaru 38, wanda aka kama a Jos, babban birnin jihar.
Wani bangare na kalaman na Nansel na cewa:
“Da ake yi musu tambayoyi, wadanda ake zargin sun amsa cewa sun hada baki wajen sayar da motar a kan naira miliyan 2.5.”
Nansel ya kara da cewa kwamishinan ‘yan sandan jihar, Maiyaki Baba, ya yabawa jami’an da suka yi aikin, sannan ya bayar da umarnin gurfanar da su a gaban kotu kamar yadda jaridar Independent ta wallafa.
'Yan bindiga sun kai hari gidan tsohon ministan yada labarai
Legit.ng a baya ta kawo rahoto da ke bayyana cewa wasu 'yan bindiga da ake zaton masu garkuwa da mutane ne sun kai hari gidan tsohon ministan yada labarai, Labaran Maku da ke karamar hukumar Akwanga ta jihar Nasarawa.
An bayyana cewa 'yan bindigar sun isa gidan da misalin karfe 7:50 na dare, inda suka kutsa kai ciki gami da yin harbe-harbe.
Asali: Legit.ng