El-Rufai: 'Yan Boko Haram, IPOB, Da ESN Na Tsoron Babban Hafsan Sojojin Najeriya Taoreed Lagbaja

El-Rufai: 'Yan Boko Haram, IPOB, Da ESN Na Tsoron Babban Hafsan Sojojin Najeriya Taoreed Lagbaja

  • Malam Nasir El-Rufai ya bayyana cewa sabon hafsan sojojin Najeriya, Taoreed Lagbaja zai yi maganin 'yan ta'adda baki daya
  • Ya ce 'yan Boko Haram, IPOB, da 'yan bindigar yankin Kudu maso Gabas na jin tsoron hafsan tsaron
  • El-Rufai ya kuma shawarci babban hafsan sojojin da ya ci gaba da jajircewa kamar yadda ya saba a baya

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya bayyana cewa 'yan Boko Haram, 'yan asalin Biafra (IPOB), da kuma 'yan bindigar Kudu maso Gabas da aka fi sani da ESN, na tsoron hafsan hafsoshin Najeriya, Taoreed Lagbaja.

Ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Lahadi, 24 ga watan Yuli.

El-Rufai ya yabawa babban hafsan sojojin Najeriya, ya ce zai magance matsalolin tsaro
El-Rufai ya ce babban Hafsan hafsoshin Najeriya Taoreed Lagbaja zai magance matsalar tsaron da ta addabi Najeriya. Hoto: Nasir El-Rufai
Asali: Facebook

Taoreed zai gama da 'yan bindiga baki ɗaya

El-Rufai ya ce yana da tabbacin cewa babban hafsan yasan aiki, kuma zai yi abinda ya kamata a yaƙi da ake da ta'addanci a Najeriya.

Kara karanta wannan

Wanda Ya San Ciki da Wajen APC, Ya Haska Kuskuren Tsohon Shugaban Jam’iyya 3

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce ko shakka ba ya yi cewa sabon babban hafsan hafsoshin zai gama da duk wasu ayyukan 'yan ta'adda, 'yan fashin daji, masu fasa bututun mai da 'yan bindiga a Najeriya baki ɗaya.

El-Rufai ya ƙara da cewa ya san sabon babban hafsan tsaron sosai, saboda shi ne shugaban sojojin Kaduna a lokacin da yake gwamnan jihar.

Yana jagorantar sojoji wajen yaƙi da 'yan ta'adda

El-Rufai ya kuma bayyana cewa Lagbaja ya kasance yana jagorantar jami'ansa zuwa cikin daji don yaƙar 'yan ta'adda a lokacin da yake Kaduna.

Ya ƙara da cewa haka kuma ya yi a lokacin da yake a Arewa maso Gabas wajen yaƙi da 'yan Boko Haram, hakan nan ma yayin da yake faɗa da 'yan Biafra da ESN.

A cikin bidiyon da El-Rufai ya wallafa haɗe da rubutun a shafin nasa na Twitter, an ga babban hafsan sojojin na bai wa sojojin umarnin su yi aiki tuƙuru don samar da zaman lafiya a jihar Filato.

Kara karanta wannan

Gwamnan Jihar Arewa Ya Koka Kan Kwararar 'Yan Ta'adda a Jiharsa, Ya Gana Da Babban Hafsan Tsaro

Daga ƙarshe El-Rufai ya roƙi babban hafsan sojojin da ya ci gaba da irin abinda ya saba yi a baya.

Sojojin Najeriya sun yi nasarar kakkaɓe 'yan ta'adda a jihohin Sokoto da Zamfara

Legit.ng a baya ta kawo muku wani rahoto kan wata gagarumar nasara da sojojin Najeriya suka samu kan 'yan ta'addan yankin Sokoto da Zamfara.

Dakarun sojin dai sun yi nasarar lalata maɓoyar 'yan ta'addan gami da halaka wasu daga cikinsu a wata arangama da suka yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng