Daukar Ma'aikata: NDLEA Ta Fitar Da Jerin Sunayen Wadanda Za Ta Dauka Aiki a Shekarar 2023

Daukar Ma'aikata: NDLEA Ta Fitar Da Jerin Sunayen Wadanda Za Ta Dauka Aiki a Shekarar 2023

  • Hukumar NDLEA ta fitar da jerin sunayen mutanen da suka yi nasarar samun guraben aikin da za ta ɗauka na bana
  • Hukumar ta buƙaci duka waɗanda sunayensu suka fito, da su hallara zuwa wuraren da za a horar da su
  • Hukumar ta kuma bayyana cewa mata masu ciki da waɗanda aka samu da shan miyagun ƙwayoyi, za su rasa damar ɗaukarsu aikin

FCT, Abuja - Hukumar Hana Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA), ta fitar da jerin sunayen mutanen da suka yi nasarar samun guraben aikin da za ta ɗauka na shekarar 2023.

Kakakin hukumar, Femi Babafemi ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a Abuja ranar Lahadi kamar yadda Daily Trust ta wallafa.

An saki sunayen wadanda aka dauka aikin NDLEA
An fitar da sunayen wadanda aka dauka aikin NDLEA a 2023. Hoto: Photo credit: Stefan Heunis/AFP
Asali: Getty Images

Ya buƙaci waɗanda sunayensu suka fito da su hallara wuraren da za a horar da su

Kara karanta wannan

Matasa Sun Kutsa Katafaren Rumbun Ajiyar Kayayyaki Na Ɗan Majalisa, Sun Tafka Ta'adi, An Rasa Rayuka a Arewa

Ya ce waɗanda aka ɗauka a matsayin jami'an bincike kan miyagun ƙwayoyi, za su je kwalejin hukumar na horar da jami'ai da ke Kotton Rikus, Jos, jihar Filato.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai kuma sauran jami'an da aka ɗauka za su je kwalejin Jami'an Tsaro na Fararen Hula (NSCDC) da ke Babbar-Ruga, kan titin Batsari, jihar Katsina domin karɓar atisaye.

Ya buƙaci duka waɗanda sunayen nasu suka fito da su tabbata sun hallara a wuraren da za a horar da su, kuma a ranakun da aka tsaida musu.

Ya kuma bayyana cewa duk wanda ya wuce karfe 6:00 na yammacin ranar 2 ga watan Agusta mai kamawa ba tare da ya hallara a wajen horaswa ba, to ya kori kansa daga aikin.

Ba za a bar mata masu juna biyu su shiga cikin atisayen ba

Kara karanta wannan

Mai Shari'a Ugo: Babban Alkalin Da Ke Jagorantar Shari'ar Neman a Soke Zaben Tinubu Ya Yi Murabus? Gaskiya Ta Bayyana

Babafemi ya kuma bayyana cewa, mata masu juna biyu ba za su samu damar shiga cikin waɗanda za a horar domin aikin ba.

Ya ce yana da kyau kowa ya sani cewa, a yayin da ake gudanar da atisayen, za a yi gwaje-gwaje da dama da suka shafi awon ciki da na shan ƙwayoyi.

Babafemi ya ƙara da cewa duk wanda aka gwada, sakamakonsa ya nuna yana shan miyagun ƙwayoyi, ko kuma juna biyu, za a kore shi daga cikin waɗanda za a ɗauka.

Sannan kuma ya buƙaci kowa ya zo da lambar shaidar zama ɗan ƙasa (NIN), takardar shaidar neman aikin, da kuma duka sauran muhimman takardu a yayin da za su je wajen atisayen.

Daga ƙarshe, ya shawarci waɗanda sunayen nasu suka fito da su duba shafin hukumar domin samun ƙarin bayani kan abubuwan da ya kamata su yi.

Majalisa ta nemi shugaba Tinubu da ya cire takunkumin ɗaukar ma'aikata a Najeriya

Kara karanta wannan

Kashim Shettima Ya Miƙa Wata Babbar Buƙata Ga Tsoffin Sanatoci Dangane Da Gwamnatin Tinubu

Legit.ng a baya ta kawo muku rahoto kan roƙon da Majalisar Wakilai ta Najeriya ta yi wa shugaban ƙasa Bola Tinubu, kan ya cire takunkumin ɗaukar ma'aikata a hukumomin gwamnati.

Majalisar ta buƙaci hakan ne domin bai wa matasan Najeriya damar cike guraben ayyukan da suke a hukumomi daban-daban na gwamnatin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng