Cire Tallafin Man Fetur: Babban Malamin Addini Ya Hango Babban Hadari Na Tafe

Cire Tallafin Man Fetur: Babban Malamin Addini Ya Hango Babban Hadari Na Tafe

  • Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, Primate Elijah Ayodele, ya hango haɗari mai girma na tunkaro manyan ƴan kasuwar man fetur
  • Malamin addinin ya bayyana cewa yakamata ƴan kasuwar su koma ga Allah a wannan lokacin ko da kuwa sun samu manyan kuɗi daga kasuwancin man fetur ɗin
  • Abinda Ayodele ya hango dai na zuwa ne a yayin da gwamnatin Tinubu ta cire tallafin man fetur sannan aka buɗe kasuwancin man fetur ɗin ga masu ruwa da tsaki

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Primate Elijah Ayodele, shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, ya hango haɗari ga masu ruwa da tsaki a kasuwancin man fetur.

A wani rubutu da ya yi a shafinsa na Twitter, malamin addinin ya buƙaci ƴan kasuwar man fetur da su koma ga Allah, domin babu abinda yake hangowa yana tunkararsu face haɗari wanda kuɗinsu ba zai iya dakatar da shi ba.

Kara karanta wannan

Tallafin Man Fetur: Taliya, Gari Da Rukunin Abubuwa 5 Da Zaka Iya Saya Da Naira 8,000

Fasto Ayodele ya yi sabon hasashe kan yan kasuwar man fetur
Fasto Ayodele ya yi hasashen hadari na tunkaro yan kasuwar man fetur Hoto: @primate_ayodele, @OfficialABAT
Source: Twitter

Ayodele ya fitar da sabon hasashe ana tsaka da jin raɗaɗin cire tallafin man fetur

Sabon hasashen na Ayodele na zuwa ne lokacin da ƴan Najeriya ke ci gaba da jin raɗaɗin cire tallafin man fetur da gwamnatin Shugaba Tinubu ta yi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Cire tallafin man fetur ɗin dai ya sauya yadda lamura ke gudana a sashin albarkatun man fetur na ƙasar nan.

Hukuncin shugaban ƙasar na tsige tallafin man fetur ya janyo ƙarin kuɗin abubuwan masarufi a ƙasar nan, wanda hakan ya taɓa yadda jama'a ke gudanar da rayuwarsu fiye da kaso 100%.

Hasashen Primate Ayodele kan manyan ƴan kasuwar man fetur

Primate Ayodele, a sabon hasashen da ya yi, ya gargaɗi ƴan kasuwar man fetur da su ji tsoron haɗarin da ke tafe musu sannan su koma ga Allah saboda kuɗin da suka samu ba za su cece su ba.

Kara karanta wannan

IPMAN Ta Bayanna Babban Dalilin Da Ya Janyo Tsadar Man Fetur a Najeriya

Rubutun nasa na cewa:

"Ina amfani da wannan lokacin domin shawartar manyan ƴan kasuwar mai a Najeriya su koma ga Allah a wannan lokacin mai muhimmanci, saboda na hango haɗari na tafe duk da suna samun babbar riba a kasuwancin man fetur."

Cire Tallafin Man Fetur Zai Bata Gwamnatin Tinubu - Ayodele

A baya rahoto ya zo cewa Primate Ayodele ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya yi gaggawa wajen cire tallafin man fetur a ƙasar nan.

Primate Ayodele ya nuna cewa cire tallafin man fetur ɗin zai ɓata sunan gwamnatin Shugaba Tinubu saboda halin da ƴan Najeriya za su tsinci kansu a ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng