Kungiyar NANS Za Ta Yi Zanga-Zanga Kan Karin Kudin Makarantu

Kungiyar NANS Za Ta Yi Zanga-Zanga Kan Karin Kudin Makarantu

  • Ƙungiyar ɗalibai ta ƙasa (NANS) ta nuna rashin amincewarta da ƙarim kuɗin makarantu da aka yi a faɗin ƙasar nan
  • Ƙingiyar NANS ta yi kira ga ɗalibai da su shirya gudanar da zanga-zanga kan ƙarin kuɗin makarantar da gwamnato ta yi
  • NANS ta buƙaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta soke tsarin ƙarin kuɗin makarantar ba tare da ɓata lokaci ba

FCT, Abuja - Ƙungiyar ɗalibai ta ƙasa (NANS) ta yi kira ga ɗalibai da su shirya gudanar da zanga-zanga kan ƙarin kuɗin makarantun gaba da sakandire da aka yi a Najeriya.

Rahotanni sun nuna cewa wasu daga cikin jami'o'in gwamnatin tarayya da na jihohi sun ƙara kuɗin makarantarsu fiye da kaso 100%, yayin da aka ƙara kuɗin makarantun 'Unity Schools' na gwamnatin tarayya daga N45,000 zuwa N100,000.

Kara karanta wannan

NULGE: Jerin Sunayen Gwamnonin Jihohi 16 Da Har Yanzu Ba Su Aiwatar da Mafi Karancin Albashi N30,000 Ba

Kungiyar NANS za ta gudanar da zanga-zanga kan karin kudin makaranta
Shugabannin NANS tare da Shugaba Tinubu Hoto: @OfficialABAT
Asali: Twitter

Ƙungiyar NANS a cikin wata sanarwa da kakakinta na ƙasa, Giwa Temitope, ta fitar ta nuna rashin dacewar ƙarin kuɗin makarantar da gwamnati ta yi, cewar rahoton The Punch.

"Abun takaici ne gwamnati za ta yi tunanin ƙara kuɗin makaranta ba tare da tunanin yadda za ta ceto sama da ƴan Najeriya mutum 133m dake fama da matsanancin talauci ba."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ƙarin kuɗin makaranta a makarantun gaba da sakandire ba abinda zai yi face ƙara yawan talauci a ƙasa da yawan yaran da basu zuwa makaranta."

Ƙungiyar NANS ta bayyana buƙatunta

A cewar ƙungiyar babu wani dalilin yin ƙarin ƙudin makarantar, rahoton Daily Trust ya tabbatar.

"Buƙatar mu a bayyana take, dole ne a dakatar da ƙoƙarin ƙara kuɗin makaranta, sannan waɗanda suka riga suka ƙara dole ne su soke ƙarin da gaggawa."
"Muna kira ga dukkanin ɗalibai ƴan Najeriya da su shirya tsaf domin gudanar da zanga-zanga kamar yadda aka yi a lokacin yajin aikin ASUU, har sai gwamnatin tarayya ta sauya wannan tsarin."

Kara karanta wannan

Mai Shari'a Ugo: Babban Alkalin Da Ke Jagorantar Shari'ar Neman a Soke Zaben Tinubu Ya Yi Murabus? Gaskiya Ta Bayyana

Jami'ar Dan Fodiyo Ta Dage Jarabawarta

A wani labarin kuma, jami'ar Usmanu Dan Fodiyo (UDUS) da ke Sokoto ta sake ɗage jarabawarta ta zangon karatu na farko har na tsawon sati ɗaya.

Jami'ar ta ɗauki matakin ɗage jarabawar ne saboda rashin biyan kuɗin makaranta daga ɓangaren ɗaliban jami'ar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng