“A Bata Karramawa Ta Kasa”: Obi Ya Jinjinawa Ma’aikaciyar Otel Da Ta Mayarwa Kwastama Da Miliyan 55

“A Bata Karramawa Ta Kasa”: Obi Ya Jinjinawa Ma’aikaciyar Otel Da Ta Mayarwa Kwastama Da Miliyan 55

  • Yan Najeriya sun yi tururuwan zuwa kafofin intanet domin jinjinawa Ms Kekwaaru Ngozi Mary, ma'aikaciyar otel din Eko Hotels & Suites wacce ta mayar wa kwastama miliyan 55 da ya batar
  • Mutane da dama sun ji dadin abun da ta yi duk da matsin tattalin arziki a Najeriya, inda yan kasarta ke shan wahala wajen siyan kayayyakin bukata na yau da kullun
  • Wannan abu da Ms Mary ta yi ya ja hankalin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party, Peter Obi, wanda ya bayyana abun da ta yi a matsayin mai tsuma zuciya

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Lagos, Lekki - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party, Peter Obi, ya jinjinawa ma'aikaciyar otel din 'Eko Hotel and Suites', wacce ta mayarwa wani kwastama kudin naira miliyan 55 ($70,000) da ya manta.

Kara karanta wannan

Ma’aikaciyar Otel Ta Tsinci Dalolin da Sun Haura N55m Amma Ta Yi Cigiya a Legas

An tattaro cewa ma'aikaciyar otel din mai suna Ms Kekwaaru Ngozi Mary, ita ce ta tsinci kudin a da bakon otel din ya batar.

Obi ya jinjinawa Ms Ngozi Mary
“A Bata Karramawa Ta Kasa”: Obi Ya Jinjinawa Ma’aikaciyar Otel Da Ta Mayarwa Kwastama Da Miliyan 55 Hoto: Mr Peter Obi/Eko Hotels & Suites
Asali: Facebook

A cewar jaridar Vanguard, Ms Mary ta tuntubi hukumar otel din, wadanda suka gaggauta mayar da kudin ga mai su.

Manajan otel din, Danny Kioupouroglou, ya bayyana abun da Mary ta yi a matsayin "shaida ga gaskiya da amincin ma'aikatanmu."

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce:

“A Otal din Eko $ Suites, muna alfahari da tsayawarmu tsayin daka a kan yin abin da yake daidai da kuma jin dadin abokin hulda. Mun yi imani cewa ma’aikatanmu su ne mafi girman jarinmu, kuma wannan lamari da ya da auku ya sake jaddada mana ra’ayin nan."

Abun da Peter Obi ya ce game da Mary

A wata wallafa da ya yi a Twitter a ranar Asabar, 22 ga watan Yuli wanda Legit.ng ta gani, Obi ya bayyana abun da Mary ta yi a matsayin mai sanyaya zuciya.

Kara karanta wannan

Ba a Tausayin Talaka: PDP Ta Yiwa Tinubu da APC Wankin Babban Bargo Kan Tsadar Mai

Ya rubuta:

“Abin farin ciki ne da kuma tabbatar da cewa duk da wahalhalun da kasar nan ke ciki da kuma gurbacewar tarbiyya a cikin al’umma, an samu rahoton cewa ma’aikacin Eko Hotel and Suites, Kekwaaru Ngozi Mary, ta mayar wa wani abokin cinikin otal din da ke Legas wasu makudan kudade da suka kai dala 70,000 da ya batar."

Ma'aikaciyar otel ta tsinci daloli a Lagas, ta yi cigiyar mai shi

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Kekwaaru Ngozi Mary ta na aiki ne a otel dinnan da yake garin Legas, Eko Hotel & Suites, a makon nan ta nuna tsantsar gaskiyarta.

Kekwaaru Ngozi Mary ta tsinci $70,000 da wani Bawan Allah ya jefar da su a otel, ita kuwa ta sa aka shiga cigiyar nemansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng