Hankalin Jama’a Ya Kara Ta’azzara, Ana Zaman Jira Yayin da Shugaba Tinubu Ke Shirin Bayyana Ministocinsa
- Ana yiwa shugaba Bola Tinubu kyakkyawan zaton cewa, haziki ne wurin mafarautar nagartattun mutane don aiki da su
- MS Ingawa, mai sharhi kan harkokin siyasa, ya ce shugaba Tinubu zai yi hobbasa wajen dauko wadanda suka dace a ministocinsa
- Ana sa ran jerin sunayen ministocin zai isa majalisar dattawa a farkon mako mai zuwa, kuma ‘yan majalisar sun bayyana shirin fara tantance wadanda aka nada
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Fatan cewa shugaban kasa Bola Tinubu zai nada nagartattun mutane a matsayin ministoci ya kara jan hankali domin an san shi wajen hazaka a mafarautar wadanda suka dace ya yi aiki da su.
MS Ingawa, wani mai sharhi kan harkokin siyasa, yayin da yake zantawa da majiyar Legit.ng, ya bayyana fatansa na cewa shugaba Tinubu zai nada nagartattun mutane, inda ya kara da cewa ya yi imanin cewa shugaban kasar zai kawo “wani abu na daban”.
Lokacin da Tinubu zai aika jerin sunayen ministoci zuwa majalisar dattawa
A farkon mako mai zuwa ne ake sa ran jerin sunayen ministocin shugaba Tinubu zai isa zauren majalisa, kuma ana sa ran fara tantance wadanda zai nadan nan take.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
An kuma bayyana cewa majalisar dattawan na shirin dakatar da hutun da take shirin tafiya na shekara, wanda ake sa ran za su fara a ranar 27 ga watan Yuli.
Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya ruwaito, wani babban jogo a majalisar dattijawa ya bayyana cewa an dakatar da batun hutun ne domin bai wa 'yan majalisar damar zama a kullumdon duba ministocin, wanda ake tunanin dage tafiya hutun da mako guda.
"Tinubu zai nada mafi kyawun mutane", Ingawa ya bayyana fatansa na gari
Shugaban kwamitin majalisar dattijai kan harkokin yada labarai da hulda da jama’a, Yemi Adaramodu, ya ce an ware isasshen lokaci da a duba bukatar shugaban kasa kan tantance ministocin.
Amma Ingawa ya ce:
"Na yi imanin cewa jerin sunayen ministocin zai kunshi 'yan siyasa da kwararru. An san BAT da zakulo haazikai da kuma sakayya ga masu biyayya. Amma na yi imanin jerin ministocin zai bambanta da wanda muka saba da shi."
Magana ta kare, majalisa ta fasa zuwa hutu saboda rashin ministocin Tinubu
A wani labarin, majalisar dattawa za ta dakatar da hutun da za ta yi na shekara saboda an ce tana sa ran ganin ministocin da shugaba Bola Tinubu ya nada domin tantance su.
Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya ruwaito, 'yan majalisar na jiran jerin sunayen ne daga fadar shugaban kasa a farkon mako mai zuwa.
Wani babban jami’in majalisar dattawan ya bayyana cewa ana sa ran majalisar ta fara hutun shekara-shekara, wanda ake sa ran zai fara daga ranar 27 ga watan Yuli zuwa Satumba.
Asali: Legit.ng