Hukumar Sojoji Ta Kaddamar Da Sabon Atisayen Kakkabe 'Yan Bindiga a Jihar Plateau

Hukumar Sojoji Ta Kaddamar Da Sabon Atisayen Kakkabe 'Yan Bindiga a Jihar Plateau

  • Hukumar sojojin ƙasa ta Najeriya ta ƙaddamar da sabon atisaya a jihar Plateau domin kakkaɓe ƴan bindigan dake tayar da zaune tsaye a jihar
  • Sabon atisayen wanda aka sanya wa sunan 'Operation Hakorin Damisa IV' an ƙaddamar da shi ne a ƙaramar hukumar Mangu ta jihar
  • Ƙaramar hukumar Mangu ta yi fama da hare-haren ƴan bindiga wanda hakan ya janyo asarar rayukan mutane masu yawa

Jihar Plateau - Hukumar sojojin Najeriya ta ƙaddamar da sabon atisayen sojoji a jihar Plateau, wanda aka sanya wa suna 'Operation Hakorin Damisa IV'.

Shugaban hukumar sojojin ƙasa, Manjo Janar Taoreed Lagbaja, shi ne ya ƙaddamar da sabon atisayen ranar Asabar, 22 ga watan Yuli a ƙaramar hukumar Mangu ta jihar Plateau, rahoton The Punch ya tabbatar.

Hukumar sojojin kasa ta kaddamar da sabon atisaye a jihar Plateau
Manjo Janar Taoreed Lagbaja da sauran hafsoshin tsaro Hoto: Nigerian Army
Asali: Twitter

Shugaban hukumar sojojin ƙasan ya bayyana cewa manufar ƙaddamar da sabon atisayen shi ne kawo ƙarshen kashe-kashen da ake yi a ƙaramar hukumar da sauran sassan jihar.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Hankula Sun Tashi Bayan Wata Katanga Ta Rufto Kan Wasu Yara, An Samu Asarar Rai

Manjo Janar Lagbaja ya buƙaci dakarun sojojin sun ƙara zage damtse

Da yake magana wajen ƙaddamar da atisayen, Manjo Janar Lagbaja, ya hori jami'an tsaron da su daƙile kowace irin barazanar tsaro a yankin da jihar Plateau baki ɗaya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ɓuƙace su da ci gaba da amsa kiran kai agaji da gaggawa inda ya ƙara da cewa yakamata su riƙa gayawa mutanen yankin halin da ake ciki dangane da ayyukansu.

A cewarsa hakan zai ƙara ƙarfafa ƙwarin gwiwar mutanen yankin kan ayyukansu.

A cikin watanni biyu da suka gabata dai an halaka sama da mutum 300 a ƙaramar hukumar Mangu da ƙauyukan dake maƙwabtaka da ita a dalilin haren-haren ƴan bindiga.

Bayan ya kammala jawabi ga dakarun sojojin da aka kawo domin gudanar da Operation Hakorin Damisa, Manjo Janar Lagbaja ya wuce wata makarantar firamare a yankin domin ganawa da manyan masu faɗa aji a yankin.

Kara karanta wannan

Rikicin APC: Tsohon Gwamna Zai Maye Gurbin Omisore a Kujerar Sakataren Jam'iyyar Na Kasa? Bayanai Sun Fito

Sojoji Sun Sheke 'Yan Bindiga a Jihar Zamfara

A wani labarin kuma, dakarun sojoji masu yaƙi da ƴan bindiga a jihar Zamfara sun samu nasarar fatattakar wasu miyagun ƴan bindiga daga maɓoyarsu.

Dakarun sojojin na atisayen 'Operation Hadarin Daji' sun kuma halaka ƴan bindiga masu yawa tare da ƙwato miyagun makamai a hannunsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng