“Zai Iya Tsawon Awanni 8”: Dan Najeriya Ya Mayar Da Motar Bus Zuwa Mai Amfani Da Wuta, Ya Kai Shi Gidan Caji
- Wani matashi ya wallafa bidiyon wata mota da ke caji a wani gidan caji bayan an sauya injin dinta
- An gano bas din tsaye a gaban mita yayin da aka makala tiyonta a gefen motar domin caja ta da wutar lantarki
- Yan Najeriya da dama da suka kalli bidiyon sun tambayi yadda za a iya sauya injin dinsu mai aiki da man fetur zuwa lantarki don rage tsadar hawa mota
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Wani mutum ya wallafa wani bidiyo na yar karamar motar bas da aka sauya ta daga injin mai amfani da mai zuwa mai amfani da wutar lantarki.
An paka motar a gaban mita kamar dai yadda ake yi a gidan mai. Wata murya da ke tashi ta karfafawa mutane gwiwar mayar da injinan motocinsu zuwa masu amfani da wutar lantarki.
Soyayya Ruwan Zuma: Bidiyon Yadda Amarya Ta Kama Wasa Da Angonta a Wajen Budar Kansu Ya Dauka Hankali
Tashar cajin motoci da wutar lantarki
An jona cajin da ke jikin mitan a wajen cajin da ke gefen motar bas din. Wani katon allo da ke gaban gidan cajin ya nuna cewa ana sanya kowani kilowatt na wuta a kan N150.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wasu mutane sun taro a wajen motar da ke caji don daukar bidiyon wannan sabuwar fasahar. A wani bidiyon, wani mutum (@charleyman8) ya yi bayanin cajin nawa motar za ta iya sha a kowani lokaci, yana mai bayyana lokacin tsakanin awanni bakwai da takwas.
Kalli bidiyon a kasa:
Jama'a sun yi martani
user9249885215630 ya ce:
"Eh lokaci ya yi da za mu fara amfani da motoci masu aiki da wutar lantarki."
user5815598716328 ya tambaya:
"Idan aka haramta motoci masu caji a nija yaya za ka yi?"
realben_nc4a ya ce:
"Kada ka manta ka siya pôwêr bank ka hada dan uwa, kada ka ce ban fadi nawa ba."
obichidubemfrankl ya tambaya:
"Me ake bukaa don sauya shi kuma yaya karkonsa yake?"
Cosmos ya ce:
"Ita wasa har sai batir dinka ya yi kasa kamar wayar Iphone a kan hanya da baida kyau."
Legit.ng ta zanta da wani mutum da ya mallaki abun hawa mai suna mallam Abubakar don jin ta bakinsa game da sauya motoci zuwa masu amfani da wutar lantarki.
Malam Abubakar ya ce:
“A matsayina na mai motar hawa da ke amfani da man fetur ina ganin idan har na samu dama zan sauya motata zuwa mai amfani da lantarki.
“Dalilina kuwa shine motoci masu amfani da lantarki za su fi saukin harka, sa’annan zai zamana akwai wuraren caji kamar yadda ake da gidajen mai sannan ba za su zamo da tsada kamar man fetur ba.
“Kuma hakan zai sa a inganta wutar lantarki. Zai kuma sa mutane su samu rara wajen siyan sauran kayan amfani tunda ba mota kadai mutum zai dunga kashewa kudi ba yadda man fetur ke kara tsada kullun.”
Dan Maiduguri Ya Kera Adaidaita Mai Aiki Da Lantarki Wanda Ka Iya Gudun 120Km Bayan Chajin Minti 30
A wani labari da daban, mun kawo cewa kyawawan hotunan adaidaita sahu masu aiki da lantarki wanda kamfanin Phoenix Renewable Limited ya kera a Maiduguri sun yadu a shafukan soshiyal midiya.
Hadaddun hotunan adaidaita sahun wanda ake yiwa lakabi da Keke Napep ya sanya yan Najeriya da dama tofa albarkacin bakunansu sannan sun bukaci gwamnati da ta tallafawa kamfanin.
Asali: Legit.ng