Benue: Mun Ceto Biliyan N1.2bn Daga Ma'aikatan Bogi, Gwamna Alia
- Gwamnan jihar Benuwai ya bankaɗo badakaloli a tsarin biyan ma'aikata albashi, ya ceto kuɗi kimanin biliyan N1.2 a wata ɗaya
- Wannan na zuwa ne kwanaki kalilan bayan gwamnatin Benuwai ta sanar da cewa ta gano ma'aikatan bogi 2,500
- Gwamna Alia ya buƙaci mazauna jihar su bai wa gwamnati haɗin kai da goyon baya don cimma nasara
Benue - Gwamnan jihar Benuwai da ke Arewa ta Tsakiya, Rabaran Hyacinth Alia, ya bayyana cewa gwamnatinsa ta yi nasarar ceto kuɗi N1.2bn daga ma'aikatan bogi.
Jaridar Vanguard ta rahoto gwamnan na cewa an ceto waɗannan kudaɗen ne a matakin farko na bincike da tsaftace tsarin biyan albashin ma'aikatan jihar.
Idan zaku iya tunawa a yan kwanaki kaɗan da suka shige, gwamnatin Benue ta sanar da cewa ta bankaɗo ma'aikatan bogi 2,500 a tsarin da ake biyan ma'aikata albashi.
Karin Bayani: Gwamnatin Uba Sani Ta Gano Sabuwar Cutar da Ta Ɓalle a Kaduna, Ta Faɗi Matakan da Ta Ɗauka
Badakalar da muka gano abin damuwa ne - Alia
Da yake jawabi ga shugabannin APC a Makurɗi a karshen makon nan, Alia ya ce. badaƙalar da ake bankaɗo wa a matakin farko na bincike babban abin damuwa ne ga kowa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Gwamnan ya kuma yi nadamar yadda matakin bincike ya haddasa jinkiri wajen biyan malaman makaranta da ma'aikatan kananan hukumomin albashinsu.
Ya kuma tabbatar da cewa a daidai lokacin da yake magana, an biya kusan kowane ma'aikaci haƙƙinsa na watan da ya gabata.
Rabaran Alia ya yi bayanin cewa wannan binciken da gwamnatinsa ta tsira ya zama tilas kuma zai amfani al'ummar jihar Benuwai.
PM News ta rahoto gwamnan na cewa:
"Zuwa yanzu gwamnati ta ceto N1.2bn daga ma'aikatan bogi 2,500 da aka cire kuma akwai wasu abubuwa da dama da muka bankaɗo."
"Abinda nake nufi shi ne a baya ana biyan N1.6bn a matsayin albashin malamai amma bayan gano badaƙalar da ke ciki yanzu miliyan N800 ne za a biya duk wata."
Gwamna Alia, wanda ya tabbatar da cewa ba zai yi ƙasa a guiwa ba sai ya toshe duk wata ƙofa da kudaɗe ke sulalewa, ya nemi mutane su ba shi haɗin kai da goyon baya.
Bayan Tsawon Lokaci, Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa Ta Zaɓi Sabon Kakaki
A wani rahoton na daban Bayan tsawon lokaci ana taƙaddama kan shugabanci, majalisar dokokin Nasarawa ta zaɓi sabon shugaba da mataimaki.
Baki ɗaya mambobi 24 na majalisar sun halarci zaman ranar Jumu'a a Lafiya, babban birnin jihar Nasarawa bayan jerin zaman sulhu tsakanin tsagin Ogazi da tsagin Balarabe.
Asali: Legit.ng