Hukumar NEMA Ta Ankarar da Al’ummar Neja Kan Ambaliyar Ruwa a Kananan Hukumomi 11
- Hukumar NEMA ta ankarar da al'ummar jihar Neja cewa za su fuskanci ambaliyar ruwa sosai a wasu kananan hukumomi 11
- Lamarin zai fi kamari a kananan hukumomin Mokwa, Shiroro, Lavun da Borgu, yayin da zai kasance tsaka-tsaki a Edati, Gbako, Wushishi, Rafi, Mashegu, Magama da Agrana
- An umurci mazauna yankunan kogi da su gaggauta barin wajen domin neman tudun tsira domin dai kogunan na dab da batsowa sakamakon cika da suka yi
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA) ta yi kira ga mazauna kananan hukumomi 11 a jihar Neja da su shirya tunkarar matsalar ambaliyar ruwa a watanni masu zuwa, jaridar Daily Trust ta rahoto.
Shugabar ofishin ayyuuka na Minna, Zainab Sa’idu, ce ta yi wannan gargadin a cikin wata sanarwa da ta fitar a garin Minna, babban birnin jihar.
Kananan hukumomi 11 za su fuskanci ambaliyar ruwa daga Yuli zuwa Nuwamba
Zainab ta bayyana cewa hasashe ya nuna cewa kananan hukumomin Mokwa, Shiroro, Lavun da Borgu na cikin rukunin yankunan da ke cikin hatsarin fuskantar ambaliyar ruwa a jihar kuma ana sa ran za su fuskanci matsanancin ambaliyar ruwa a cikin watannin Yuli zuwa Nuwamba.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ta ce kananan hukumomin Edati, Gbako, Wushishi, Rafi, Mashegu, Magama da Agrana na cikin rukunin da za su fuskanci matsakaicin ambaliyar ruwa, cewa mazauna yankin za su yi fama da ambaliyar ruwa sosai daga Yuli zuwa Nuwamba.
“Ya kamata a lura cewa jihar Neja ta riga ta fara fuskantar ambaliyar ruwa da iska mai karfi a wasu daga cikin wadannan yankuna don haka akwai bukatar al’ummar jihar su yi taka-tsan-tsan don gujewa asarar dukiyoyi da asarar rayuka,” inji ta.
An kula da gyara magudanan ruwa
Ta shawarci mazauna wadannan kananan hukumomi da aka lissafa da su tabbata sun tsaftace magudanar ruwa don gudun toshewar hanyoyin ruwa.
Ta kuma bayyana cewa ya kamata wadanda ke zaune a wuraren da ake fuskantar ambaliyar ruwa da kusa da rafi su gaggauta barin yankunan sannan su koma wuraren da suka fi tudu da tsaro.
Zainab ta kara da cewa:
“Akwai alama mai karfi da ke nuna cewa ruwan da ke kusa da kogin Neja yana karuwa kuma hakan zai kara yawan ruwan da ke cikin magudanan ruwa, saboda haka ya haifar da ambaliya a gabar kogin, wanda zai yi tasiri sosai a muhallan da ke kewayen kogunan."
Hukumar NEMA ta lissafa jerin jihohin da za a yi ambaliyar ruwa
A baya Legit.ng ta rahoto cewa hukumar NEMA mai bada agajin gaggawa ta jero wasu garuruwa a jihohin Najeriya da ake da yiwuwar fuskantar ambaliya.
An samu labari cewa amabliyar ruwan da za ayi fama da ita a shekarar nan. Za ta shafi jihohi 14.
Asali: Legit.ng