PSC Ta Kori Manyan Jami'an Yan Sandan Najeriya 3 Kan Rashin Ladabi
- Hukumar PSC ta amince da korar wasu manyan jami'an hukumar yan sandan Najeriya sakamakon aikata manyan laifuka
- Haka nan kuma hukumar ta rage wa wasu yan sanda 5 matsayi, ta tsawatarwa wasu 14 kana ta raba wa wasu Bakwai takardun gargaɗi
- Mai magana da yawun PSC, Ikechukwu Ani ne ya bayyana haka a karshen taron hukumar karo na 21 a Abuja
FCT Abuja - Hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda ta kasa (PSC) ta amince da korar wasu manyan jami’an ‘yan sanda uku bisa wasu manyan laifuka rashin ɗa'a suka aikata.
Leadership ta tattaro cewa hukumar ta kuma amince da rage wa wasu 'yan sanda biyar mukamai bayan gano suna wasa a gudanar da ayyukansu.
Mai magana da yawun hukumar PSC, Ikechukwu Ani, ne ya bayyana haka yayin da ya yake ƙarin haske kan abinda aka tattauna a taron hukumar karo na 21.
Bidiyon Dala: Wankin Hula Na Neman Kai Ganduje Dare, Yayin Da Gwamnatin Kano Ta Yo Hayar Babban Lauya
Taron wanda ya gudana ƙarƙashin jagorancin shugaban PSC, Dakta Solomon Arase, ya ƙarkare ranar Alhamis, 20 ga watan Yuli, 2023.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Waɗanne manyan jami'ai hukumar ta kora daga aiki?
Jami’an ‘yan sandan da hukumar PSC ta kora dai sun hada da mataimakan Sufuritandan ‘yan sanda (DSP) biyu da kuma mataimakin Sufeton ‘yan sanda (ASP).
Babban Sufuritandan na ’yan sanda (CSP) guda ɗaya, Sufuritanda (SP), Mataimakin Sufuritanda (DSP) ɗaya da mataimakan Sufuritandan ‘yan sanda (ASP) guda biyu an rage musu mukami saboda rashin da’a.
PSC ta hukunta jami'ai 14 da tsawatarwa mai tsanani, ta tsawarta wasu yan sanda 6, kana wasu Bakwai kuma sun samu wasiƙun gargaɗi, kamar yadda Vanguard ta tattaro.
PSC ta dawo da wasu jami'ai da aka kora a baya
Hukumar ta kuma maido da wasu jami’ai shida da aka kora daga aiki bayan hukuncin kotu ya ba su gaskiya ko kuma an sake duba kararrakinsu.
A ranar Laraba 18 ga watan Yuli ne dai hukumar ta amince da nadin mataimakin sufeto-janar na ‘yan sanda biyu, Mathew Akinyosola da Slyverster Abiodun Alabi.
Emefiele: Za'a Gurfanar da Dakataccen Gwamnan CBN a Gaban Kotu
A wani rahoton na daban Babbar Kotun tarayya ta sanya ranar 25 ga watan Yuli, 2023 domin gurfanar da dakataccen gwamnan babban banki (CBN).
Za a gurfanar da Emefiele a gaban Kotun ne domin fuskantar shari'a kan tuhumar mallakar haramtattun makamai.
Asali: Legit.ng