Kotu Ta Umarci Abba Gida Gida Ya Biya Diyyar N2m Ga Wasu Mutane 2 Da Rusau Ya Shafa A Kano

Kotu Ta Umarci Abba Gida Gida Ya Biya Diyyar N2m Ga Wasu Mutane 2 Da Rusau Ya Shafa A Kano

  • Babbar kotun Tarayya a jihar Kano ta umarci gwamnatin jihar ta biya diyyar N2m ga wasu wadanda rusau ya shafa a birnin Kano
  • Saminu Shehu da Tasiu Shehu sun shigar da karar bayan gwamnatin jihar ta saka jan layi a gininsu da ke unguwar Salanta
  • Wadanda ake zargi a karar sun hada da gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf da kwamishinan shari’a da kuma ma’aikatar filaye

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Kano – Babbar kotun Tarayya da ke jihar Kano ta umarci gwamnatin jihar ta biya kudin diyya har Naira miliyan biyu ga wasu mutane da aka rusawa dukiyoyi.

Kotun ta ba da umarni cewa gwamnatin ta biya Naira miliyan dai-dai ga wasu mutane biyu Saminu Shehu da kuma Tasiu Shehu saboda rusau da ta shafesu a unguwar Salanta da ke birnin Kano.

Kara karanta wannan

Cire Tallafi: Gwamnati Ta Yi Niyyar Saukakawa Mutane Rayuwa, Za Ta Sauya Amfani Da Fetur Zuwa Wani Abu

Kano: Kotu Ta Tilasta Abba Gida Gida Biyan Diyyar N2m Ga Wasu Mutane Da Rusau Ya Shafa
Babbar Kotun Tarayya Ta Umarci Abba Kabir Yusuf Ya Biya Diyyar N2m Kan Rusau: Hoto: Facebook.
Asali: Facebook

Wadanda suka shigar da karar ta bakin lauyansu, Bashir Ibrahim inda suka bukaci a biya su N50m kudin barna da aka musu da kuma tauye hakkinsu na ‘yan Adam, cewar Vanguard.

Wadanda aka shigar karar a gaban kotun

Wadanda ake karar sun hada da kwamishinan shari’a na jihar Kano da gwamna Abba Kabir Yusuf sai kuma ma’aikatar filaye da kula da tsare-tsare.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sauran sun hada da jami’an ‘yan sanda da kwamishinan ‘yan sandan jihar da babban sifetan ‘yan sanda, Daily Nigerian ta tattaro.

Lauyan wadanda ake kara Musa Dahiru ya fadawa kotu cewar filayen da ake magana a kansu na Kwalejin Fasaha ta jihar ce don haka yake rokon kotu da ta yi fatali da karar.

Ta umarci Abba Kabir ya cire jan layin tare da yin sabon fenti

Kara karanta wannan

Ingila Na Shirin Karbewa Tsohon Gwamnan Najeriya Naira Biliyan 100 a Kotu

Alkalin kotun, Simon Ameboda ya ce saka jan layi akan dukiyarsu don rusawa ba tare da bin ka’ida ba ya sabawa ‘yancin da suke da shi a matsayinsu na ‘yan kasa, Daily Trust ta tattaro.

Ya ce yadda aka shiga cikin gidajen nasu da tsakar dare ya sabawa ‘yancinsu na ‘yan kasa kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanadar.

Ya umarci gwamnatin da ta sake yi wa katangar tasu fenti da kuma cire jan fenti da ta saka na hukumar kula da birane.

Rusau: NITP Ta Gargadi Abba Gida Gida Kan Rushe-rushe, Ta Bayyana Asarar Da Aka Yi

A wani labarin, Kungiyar Masu Tsara Birane (NITP) ta gargadi gwamnatin jihar Kano kan ci gaba da rushe-rushe.

Abba Kabir ya dukufa wurin rushe gidaje da shagunan mutane da ya ke ganin ba a mallake su ko gina su bisa ka'ida ba.

Kungiyar ta yi Allah wadai da irin haka inda ta bayyana cewa a yanzu haka an yi asarar fiye da N120bn.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.