Jerin Sunayen Gwamnonin da Ba Su Fara Biyan Mafi Karancin Albashin N30,000 Ba Ya Bayyana

Jerin Sunayen Gwamnonin da Ba Su Fara Biyan Mafi Karancin Albashin N30,000 Ba Ya Bayyana

  • Ƙungiyar ma'aikatan kananan hukumomi a Najeriya (NULGE) ta nuna rashin jin daɗinta kan yadda ake wa mambobin cin kashi
  • NULGE ta yi Allah wadai da wasu gwamnatocin jihohi saboda har yanzun ba su aiwatar da tsarin mafi ƙarancin albashi N30,000 ba
  • Ƙungiyar ta nuna takaicinta musamman yadda har yau jihar Zamfara ba ta aiwatar da tsohon mafi karancin albashi N18,000 ba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT Abuja - A ranar 18 ga watan Afrilu, 2019, tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya rattaɓa hannu kan kudirin sabon tsarin mafi ƙarancin albashi N30,000 ya zama doka.

A wancan lokacin, gwamnatin tarayya ta ce dokar ta tilasta wa dukkan masu ma'aikata a bangaren gwamnati ko masu zaman kansu su biya mafi ƙaranci N30,000, kamar yadda Premium Times ta rahoto.

Mafi karancin albashin ma'aikata N30,000.
Jerin Sunayen Gwamnonin da Ba Su Fara Biyan Mafi Karancin Albashin N30,000 Ba Ya Bayyana Hoto: Klaus Vedfelt
Asali: Getty Images

Har yanzu jihohi 16 ba su aiwatar da mafi ƙarancin albashi ba

Kara karanta wannan

Labari Mai Daɗi: Shugaba Tinubu Ya Sake Magana Mai Jan Hankali Kan Matsalar Tsaron Najeriya

Shekaru 4 bayan rattaɓa hannu kan kudirin dokar, har yanzu wasu jihohi ba su aiwatar da dokar ba, lamarin da ya fusata ƙungiyar ma'aikatan kananan hukumomi (NULGE).

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A wata sanarwa da ta karanta a karshen taron majalisar tattalin arziƙi (NEC) ranar Alhamis, NULGE ta ankarar da cewa har yau akwai jihohin da basu aiwatar da mafi ƙarancin albashi N30,000 ba.

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa ƙungiyar ta nuna matuƙar damuwarta kuma ta ɗiga jan fenti kan jihar Zamfara a matsayin jiha mafi muni game da rashin bin mafi ƙarancin albashi.

Sanarwan ta ce:

"NULGE ta yi Allah wadai da matakin jihohin Ribas, Kuros Riba, Anambra, Imo, Enugu, Kaduna, Kogi, Kwara, Adamawa, Sokoto, Yobe, Borno, Abiya Bayelsa da Gombe bisa rashin fara biyan mafi ƙarancin albashi N30,000."
"Mafi lalacewar cikinsu ita ce jihar Zamfara, jihar da har yanzun ba ta aiwatar da N18,000 a matsayin mafi ƙarancin albashin ma'aikata ba."

Kara karanta wannan

"Babu N8,000" Cikakken Jerin Garaɓasa 6 da FG Ke Shirin Raba Wa 'Yan Najeriya Don Rage Raɗaɗi

Bayan haka NULGE ta buƙaci gwamnatin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ta ƙara mafi karancin albashi da kaso 300%, kamar yadda The Cable ta rahoto.

Jerin sunayen gwamnoni da magadansu, waɗanda har yanzu basu aiwatar da N30,000 ba

1) Cross River - Farfesa Ben Ayade/Bassey Otu

2) Rivers - Nyesom Wike/Siminalayi Fubara

3) Anambra - Farfesa Charles Soludo

4) Imo - Hope Uzodinma

5) Enugu - Ifeanyi Ugwuanyi/Peter Mbah

6) Kaduna - Nasir El Rufai/Uba Sani

7) Kogi - Yahaya Bello

8) Kwara - AbdulRahman AbdulRasaq

9) Adamawa - Ahmadu Fintiri

10) Sokoto - Aminu Tambuwal/Ahmad Aliyu

11) Yobe - Mai Mala Buni

12) Borno - Farfesa Babagana Umara Zulum

13) Abia Alex Otti/Okezie Ikpeazu

14) Bayelsa - Douye Diri

15) Gombe - Muhammad Inuwa Yahaya

16) Zamfara - Bello Matawalle/Dauda Lawal.

Gwamnoni 11 Sun Ziyarci Tsohon Shugaban APC Ta Kasa, Abdullahi Adamu

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Gwamnatin Uba Sani Ta Gano Sabuwar Cutar da Ta Ɓalle a Kaduna, Ta Faɗi Matakan da Ta Ɗauka

A wani labarin na daban kuma Gwamnoni 11 na jam'iyyar APC sun ziyarci tsohon shugaban jam'iyya, Sanata Abdullahi Adamu a gidansa da ke Abuja.

Tawagar gwamnonin, waɗanda suka roƙi tsohon gwamnan da ya ci gaba da mara wa APC baya, sun shafe kusan awa guda a gidansa suna gana wa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262