'Yan Sanda A Kano Sun Bazama Neman Makerar Masu Kera Wukake Da Ake Ta'addanci Da Su
- Jami'an 'yan sandan jihar Kano ta bazama neman makera da ke kera makamai ga wasu bata gari
- Kwamishinan 'yan sandan jihar, Muhammad Gumel shi ya bayyana haka yayin ganawa da 'yan jaridu a Kano
- Ya shawarci makeran da su tabbatar da suwa suke kerawa wukaken don kada su fada hannun bata gari
Jihar Kano - Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta bazama neman makera a jihar da ke kera makamai ga masu aikata laifuka daban-daban.
Kwamishinan 'yan sandan jihar, Muhammad Gumel shi ya bayyana haka yayin ganawa da 'yan jaridu a Kano.
Ya ce jami'ansu sun himmatu wurin tarwatsa masu aikata laifuka daban-daban a dutsen Dala da ke karamar hukumar Dala a jihar Kano, cewar Punch.
Ya koka kan yadda makeran ke hada wukake da suke fadawa hannun bata gari
A cewarsa kamar yadda PM News ta tattaro:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Kuna ganin yadda wukaken nan suke, duk wanda ke kera wadannan kasan ba na amfanin gida ba ne, sai dai aikata laifuka.
"Irin wadannan wukake idan ka duba karshensu za ka ga jami'an tsaron 'yan sanda da sojoji ne kawai ya kamata su yi amfani da su.
"Makera suna kera wadannan wukake ba tare da duba illarsu ga al'umma ba, damuwarsu su siyar saboda kudi.
"Yayin da masu aikata laifuka ke amfani da su wurin jiwa mutane raunuka har ma da kashe su idan ba su mika abin da ake bukata ba."
Gumel ya tura sakon gayyata don ilmantar da su akan aikinsu
Kwamishinan ya ce ya tura sakon gayyata ga makera don wayar musu da kai akan illar kerawa jama'a irin wadannan wukake, Vanguard ta tattaro.
Ya kara da cewa:
"Idan kwastoma ya zo wurinku ya kamata ku binciki sana'arsa ko mahauci ko wani abu daban, don sanin abin da zai yi da shi."
Rusau: Dubu ta Cika, 'Yan Sanda Sun Kama Mutane 57 Bisa Zargin Dibar Ganima
A wani labarin, jami'an 'yan sanda a jihar Kano sun cafke wasu mutane da ake zargi da dibar ganima.
Ana zargin mutanen da sace dukiyoyin al'umma a lokacin rushe-rushen gidaje da shagunan jama'a da ake rusawa.
Rahotanni sun tabbatar da cewa rundunar ta kama karin mutane 57 da ake zargi da wuce gona da iri da kuma satar dukiyar mutane.
Asali: Legit.ng