Kasar Ingila Na Shirin Karbewa Tsohon Gwamnan Najeriya Naira Biliyan 100 a Kotu

Kasar Ingila Na Shirin Karbewa Tsohon Gwamnan Najeriya Naira Biliyan 100 a Kotu

  • Ana shari’a a kotun Landan tsakanin James Ibori wanda ya yi Gwamna a Najeriya da kasar Birtaniya
  • Wani jami’in kasar Turan ya shigar da kara a kotu, yana so a karbe $129m daga asusun ‘dan siyasar
  • Idan an samu Ibori da laifi, zai zama mahukantar kasar wajen sun same shi rashin gaskiya sau biyu

United Kingdom - Wani jami’in gwamnatin Birtaniya mai gurfanar da wadanda ake tuhuma da laifi ya shigar da karar James Ibori gaban kotu.

Reuters ta rahoto cewa jami’in ya roki wata kotu da ke zama a Landan a kasar Ingila, ta bada umarnin karbe wasu kudi daga asusun James Ibori.

Fam miliyan £100 ($129m) ne adadin dukiyar da ake magana a kan su, a halin da ake ciki a Najeriya, kudin sun haura Naira biliyan 102 kenan.

Kara karanta wannan

Zargin Daukar Nauyin Ta’addanci: Kotu Ta Hana Lauyoyi Da Yan Jarida Sauraron Shar’ar Tukur Mamu

James Ibori
Tsohon Gwamna James Ibori da Bola Tinubu Hoto: independent.ng
Asali: UGC

Sabuwar shari'a a kotun Landan

Bayan dogon lokaci ana ta tataburza ta fuskar shari’a a dalilin jinkirin kotu, Birtaniya ta na daf da cin ma nasara wajen karbe wadannan tuli dukiya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Alkali David Tomlinson na kotun Southwark ya samo sababbin hujjoji kan zargin satar, abin da ba zai yi wa lauyoyin 'dan Najeriyan dadi ba.

A zaman kotun da aka yi ranar Alhamis, jaridar Punch ta ce kowane bangare ya fadin abin da yake ganin ya kamata a karbe daga lissafin da aka yi.

£101.5 ko zaman gidan kaso

Jonathan Kinnear ya shaidawa kotun Dala miliyan £101.5 ya dace a karbe, idan ba haka ba kuwa Ibori zai yi shekaru biyar zuwa 10 a kurkuku.

Ibori wanda yana Najeriya a yanzu, ya shaidawa manema labarai cewa zai kalubalanci hukuncin, yana mai fatan Alkali ya ba shi gaskiya.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tarayya, Gwamnoni Za Su Raba Kudin Da Ya Fi Kowane Yawa a Tarihin FAAC

Zaman Ibori a gidan yarin Turai

Kafin yanzu an taba shari’a da Ibori a Birtaniya, har aka daure shi a gidan yari na shekara da shekaru saboda zargin ya saci kudin mutanen jiharsa.

Daga Dubai aka wuce da ‘dan siyasar zuwa Landan inda Alkali ya same shi da laifin sata.

A sakamakon samun shi da laifuffuka 12 a shekarar 2012 ne aka yanke masa dauri a gidan gyaran hali, Duniya ta yabawa hukuncin da aka yi a lokacin.

Nada mukamai a Osun

An ji labari Ademola Adeleke ya ba kan shi mukami, ya kuma tuna da matar ‘danuwansa da ya rasu da yaron tsohon Gwamna Isiaka Adeleke.

Yaron ‘danuwan Gwamnan mai-ci da yake da shekara 20 a Duniya ya samu babban mukami a gwamnatin jihar Osun shekaru biyu da kammala jami'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng