Tallafin Tinubu: Rukunin Abubuwa 5 Da Zaka Iya Saya Da Naira 8,000 a Najeriya
A cikin 'yan kwanakin nan ne dai shugaban ƙasa Bola Tinubu ya aika da takardar neman izinin ciyo bashin dala miliyan 800 zuwa ga Majalisar Dattawa.
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Tinubu ya ce zai yi amfani da bashin da zai ciyo daga bankin duniya, wajen sayo kayan tallafi domin ragewa 'yan Najeriya raɗaɗin da cire tallafin man fetur ya jefa su ciki.
Shugaba Tinubu dai ya sanar da cire tallafin man jim kaɗan da hawansa kan karagar mulki.
Tinubu ya ce ana ƙara azurta wasu tsirarun mutane da tallafin na man fetur da ake bayarwa.
Hakan ya janyo tashin gwauron zabin farashin man fetur zuwa naira 540 duk lita ɗaya.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Bayan ƙorafe-ƙorafe da 'yan Najeriya suka yi, gwamnatin ta sanar da cewa za ta riƙa bai wa mutane miliyan 12 naira 8,000 a duk wata har na tsawon watanni shida.
Sai dai duk da haka gwamnatin ba ta tsira ba, domin kuwa 'yan Najeriya sun soki ƙudurin, inda suka koka kan cewa babu wani abu da N8,000 za ta iya yi wa mutum a halin da ake ciki.
Mun tattaro muku rukunin wasu kayayyakin amfani na gida guda 5 da mutum zai iya saya da N8,000, cikin wani rahoto da jaridar Daily Trust ta haɗa kan farashin kayayyaki a kasuwa.
Wake, Shinkafa da kuma Gari
A binciken da aka gudanar, an gano cewa da naira 8,000 zaka iya samun kwano biyu na shinkafa, kwanon wake ɗaya da kuma kwano ɗaya da rabi na garin kwaki.
Doya, Fulawa da garin Semovita
Da naira 8,000 zaka iya samun doya guda biyu, kwano ɗaya da rabi na fulawa da kuma ɗan ƙaramin buhu mai nauyin kilogiram biyu na garin Semovita.
Manja, Man girki da kuma kayayyakin ƙamshi
Da naira 8,000 zaka iya sayan kwalabe uku na manja, uku na man girki, fakiti biyu na kayan ƙamshi.
Taliyar Indomie, Spaghetti, da Macaroni
Naira 8,000 za ta iya sayawa mutum fakitin Indomie 13, ledar spaghetti shida da kuma ta Macaroni ma guda shida kamar yadda Daily Trust ta tattara.
Sukari, Ganyayyakin shayi, Madara da Manbita
Duk a cikin naira 8,000, mutum zai iya samun kwano ɗaya na sukari, kwali uku na ganyayyakin shayi, gwangwani biyu na madara da kuma gwangwanin Manbita mai nauyin giram 500.
Tinubu ya gana da jiga-jigan Najeriya kan halin da talakawa ke ciki
Legit.ng a baya ta kawo rahoton zaman da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya yi da manyan shugabannin Najeriya domin duba yadda za a shawo kan matsalar da talakawan ƙasar ke ciki.
A daren ranar Laraba, 19 ga watan Yuli ne shugaban ya gana da Shettima, Akpabio da wasu gwamnoni don tattauna yadda za a raba kayan tallafi ga 'yan Najeriya.
Asali: Legit.ng