Babban Basarake, Chief Esogban Na Benin Ya Kwanta Dama Yana da Shekaru 93

Babban Basarake, Chief Esogban Na Benin Ya Kwanta Dama Yana da Shekaru 93

  • Wani babban basaraken Benin a jihar Edo, Chief David Edebiri, ya riga mu gidan gaskiya yana da shekara 93 a duniya
  • Marigayi Esogban na Benin ya rasu ne ranar Alhamis a wani Asibitin Kuɗi da ke Benin bayan fama gajeruwar rashin lafiya
  • Wata majiya ta bayyana cewa kwanakin baya Basaraken ya ji baya jin daɗin jikinsa aka kai shi Asibiti kuma rai ya yi halinsa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Benin City, Edo - Fitaccen basaraken gargajiya mai daraja, Esogban na Benin, Chief David Edebiri, ya riga mu gidan gaskiya yana da shekaru 93 a duniya.

Rahoton Daily Trust ya tattaro cewa Chief Esogban ya mutu ne ranar Alhamis, 20 ga watan Yuli, 2023 a wani asibitin kuɗi da ke Benin, babban birnin jihar Edo.

Marigayin basaraken Benin, Chief David Edebiri
Babban Basarake, Chief Esogban Na Benin Ya Kwanta Dama Yana da Shekaru 93 Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Haka zalika rahotanni sun bayyana cewa marigayin ya cika ne bayan fama da gajeruwar rashin lafiya a Asibitin.

Kara karanta wannan

Yadda Zulum Ya Mamayi Ma’aikatan Lafiya, Ya Ziyarci Asibiti Cikin Tsakar Dare

Basaraken wanda ake wa laƙabi da 'Esogban' shi ne ya gaji Iyase (watau Firaminista) na Benin wanda aka fi sani da Odiownere na masarautar Benin.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Karo na ƙarshe da aka ga babban basaraken ya fito bainar jama'a shi ne lokacin zaben gwamna da mambobin majalisar dokoki wanda ya gudana ranar 18 ga watan Maris, 2023.

A wannan lokacin ne jama'a suka ga Basaraken yayin da ya fito kuma ya kaɗa kuri'arsa kamar kowa a akwatun zaɓensa.

Iyalan Basaraken sun tabbatar da rasuwar

Wata majiya daga cikin iyalan mamacin ta tabbatar da rasuwar Chief David Edebiri da misalin ƙarfe 12:20 na tsakar rana.

"Lokacin da Chief Esogban ya ji baya jin daɗin jikinsa, muka kai shi asibiti kwanaki kalilan da suka wuce, amma rai ya yi halinsa da tsakar ranar nan," inji shi.

Kara karanta wannan

Zulum Ya Sanya Magidanta 13,000 Farin Ciki a Jihar Borno Yayin Da Ya Yi Musu Gagarumar Kyauta

Majiyar ta ƙara da cewa iyalan marigayin zasu bari a bi matakan da ya dace wajen sanar da rasuwarsa a hukumance, kamar yadda rahoton Punch ya tattaro.

Marigayi Chief Edebiri wanda ya yi aiki da gidan jaridar Daily Times ya rubuta litattafai biyu a zamanin rayuwarsa a shekarar 2022.

'Yan Bindiga Sun Kai Farmaki Cikin Fada, Sun Halaka Babban Sarki a Najeriya

A wani labarin kuma Migayun yan bindiga sun kutsa kai har cikin fada, sun harbe basarake har lahira a jihar Imo.

Rahotanni sun nuna cewa Marigayi sarkin ya karɓi bakuncin wani mai suna, Chief Ignatius Nwaru, yana tsaka da sauraron bakon lokacin da maharan suka kutsa kai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262