IPMAN Ta Ce Tashin Dala Ne Ya Janyo Tsadar Farashin Man Fetur a Najeriya
- Kungiyar dillalan man fetur man fetur ta Najeriya (IPMAN), ta bayyana dalilin tsadar man fetur a Najeriya
- Kungiyar tashin da dalar Amurka ta yi ne ya janyo tsadar man fetur ɗin da ake fama da ita a yanzu
- Jami'in hulɗa da jama'a na IPMAN, Yakubu Suleiman ne ya bayyana haka a lokacin da yake tsokaci kan tsadar man
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jami’in hulɗa da jama’a na kungiyar dillalan man fetur ta ƙasa (IPMAN), Yakubu Suleiman ya faɗi ainihin dalilin da ya janyo tsadar man fetur a Najeriya.
Ya ɗora alhakin carkewar farashin na man fetur kan tsadar da dalar Amurka ta yi.
Ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi da gidan talabijin na Arise TV dangane da hauhawar farashin man da aka samu a cikin 'yan kwanakin nan.

Kara karanta wannan
Mai Shari'a Ugo: Babban Alkalin Da Ke Jagorantar Shari'ar Neman a Soke Zaben Tinubu Ya Yi Murabus? Gaskiya Ta Bayyana

Source: UGC
Ana amfani da dala wajen sayo mai daga ƙasar waje
Yakubu ya ce ana amfani da dalar Amurka ne wajen shigo da man fetur da sauran abubuwan da ke da alaƙa da shi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya ƙara da cewa dole ne mai ya yi tsada a gida Najeriya a duk lokacin da ɗanyan man ya yi tsada a kasuwannin duniya.
Yakubu ya ce a saboda haka farashin man fetur ɗin zai sauka daga lokacin da farashin ɗanyan man ya yi sauƙi.
Yan kasuwar mai ba sa jin daɗin tsadar man da ake fama da ita
Yakubu ya ce mutane da dama na tunanin cewa, 'yan kasuwa na jin daɗin tsadar man fetur da ake fama da ita a halin yanzu.
Ya ce babu wani ɗan kasuwa da ke jin daɗin farashin da ake sayar da man fetur a yanzu kamar yadda Daily Trust ta wallafa.

Kara karanta wannan
Wani Kamfanin Jigilar Man Fetur Ya Karya Ƙwarin NNPC, Ya Yi Abinda Kowa Ya Gaza Yi a Baya
Ya kuma ƙara da cewa a yanzu haka 'yan kasuwa na shigo da man fetur a kan N565 duk lita daga ƙasar waje.
Daga ƙarshe ya bayyana cewa duk da wannan tsadar ta fetur da ake fama da ita, Najeriya na daga cikin ƙasashen da ke shan mai da arha a Afrika.
An gudanar da zanga-zanga a Majalisar tarayya kan cire tallafin man fetur
Legit.ng a baya ta kawo rahoto kan wata zanga-zanga da ta ɓarke a Majalisar Tarayya kan cire tallafin man fetur.
Masu zanga-zangar sun nuna goyon bayansu ga matakin da Shugaba Tinubu ya ɗauka na cire tallafin man fetur jim kaɗan bayan hawansa mulki.
Asali: Legit.ng