Gwamnatin Benue Ta Bankado Ma'aikatan Bogi 2,500 Daga Fara Bincike
- Gwamnatin jihar Benuwai ta cire ma'aikata 2,500 daga tsarin biyan albashi bayan gano cewa baki ɗayansu na bogi ne
- Gwamna Alia ne ya bayyana haka a wata sanarwa da babban sakatarensa ya fitar ranar Alhamis a Makurɗi, babban birnin jiha
- Ya ce an gano bakaƙalar kudade da yawa a matakin farko na tantance ma'aikata da tsaftace tsarin biyan malaman makaranta albashi
Benue state - Gwamnan jihar Benuwai, Hyacinth Alia, ya bayyana cewa gwamnatinsa ta bankaɗo ma'aikatan bogi 2,500 a matakin farko na fara bincike.
Gwamna Alia ya ce an gano waɗan nan ma'aikatan ƙaryan ne yayin gudanar da bincike a kan tsarin biyan albashin malamai da ma'aikatan ƙananan hukumomi.
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa hakan na ƙunshe a wata sanarwa da babban sakataren gwamna Aliya, (CPS) Tersoo Kula, ya fitar ranar Alhamis a Makurɗi.
Mai Shari'a Ugo: Babban Alkalin Da Ke Jagorantar Shari'ar Neman a Soke Zaben Tinubu Ya Yi Murabus? Gaskiya Ta Bayyana
Gwamnan ya ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"A matakin farko na tantance ma'aikata da binciken tsarin biyan albashin malaman makarantun Firamare da Sakandire da ma'aikatan kananan hukumomi, an gano ma'aikatan bogi 2,500."
"Tuni aka tsaftace tsarin biyan albashi kuma dukkan ma'aikatan bogi da aka bankaɗo an cire su daga tsarin waɗanda ake tura wa albashin wata-wata."
"Gwamnati ta kuma bankado makaratun bogi, da cin ɗuri biyu, ɗaukar aiki ba bisa ka'ida ba, albashin ma'aikata, biyan matattu ko wadanda suka yi ritaya, da kuma maye gurbinsu ba bisa ka'ida ba."
Meya haddasa jinkiri wajen biyan ma'aikata albashi?
Gwamna Alia ya nuna nadama kan tsaikon da aka samu wajen biyan albashin malaman firamare da Sakandire da kuma ma'aikatan ƙananan hukumomin jihar Benuwai.
Ya ce an dauki matakin jinkirin biyan albashin ne bayan da gwamnati ta gano rashin sanin yakamata na biyan albashin ma’aikata da kuma badaƙalar makudan kudade da ake tafkawa a biyan albashin.
Ya kuma tabbatar wa ma'aikatan da aka gama tantancewa cewa zasu ga albashinsu kafin karshen wannan makon, rahoton Vanguard ya tabbatar.
Gwamna Alia na jam'iyyar APC ga gaji tsohon gwamna Samuel Ortom na jam'iyyar PDP bayan lashe zaben gwamna a ranar 18 ga watan Maris, 2023.
Shetimma, Gwamnoni da Sauran Mambobin NEC Sun Sa Labule a Villa
A wani labarin kuma Majalisar kula da harkokin tattalin arzikin ƙasa (NEC) na gana wa yanzu haka a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
SGF da gwamnonin jihohi 36 sun halarci zaman wanda mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ke jagoranta.
Asali: Legit.ng