Shettima Na Jagorantar Taron NEC Bayan Kara Farashin Fetur a Najeriya

Shettima Na Jagorantar Taron NEC Bayan Kara Farashin Fetur a Najeriya

  • Majalisar kula da harkokin tattalin arzikin ƙasa (NEC) na gana wa yanzu haka a fadar shugaban kasa da ke Abuja
  • Taron zai maida hankali kan batutuwan da suka shafi rage wa ma'aikata radadin cire tallafin man fetur
  • SGF da gwamnonin jihohi 36 sun halarci zaman wanda mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ke jagoranta

FCT Abuja - Majalisar ƙoli ta tattalin arziki a Najeriya (NEC) karkashin jagorancin mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, na gana wa yanzu haka a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Wannan taron na ranar Alhamis, 20 ga watan Yuli, 2023 na zuwa ne awanni 48 bayan kamfanin mai na kasa (NNPCL) ya ƙara farashin litar man fetur daga N540 zuwa N617.

Taron majalisar tattalin arziki NEC.
Shettima Na Jagorantar Taron NEC Bayan Kara Farashin Fetur a Najeriya Hoto: Kashim Shettima
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta rahoto cewa wannan ƙari ya tada hankalin yan Najeriya yayin yan kasuwa suka fara fargabar lamarin ka iya jawo rasa ayyuka da mutuwar sana'o'i.

Kara karanta wannan

Sauki Ya Zo: Shugaba Tinubu Ya Gana Da Manyan Kusoshi a Kasar Nan Domin Tsamo Talaka Daga Halin Kunci, Bayanai Sun Fito

Mataimakin shugaban ƙasa ne ke jagorantar taron, wanda aka fara da misalin ƙarfe 11:35 na safiyar nan bayan gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun ya buɗe da addu'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Muhimman batutuwan da NEC zata tattauna a taron yau

Mahalarta taron zasu maida hankali kan muhimman batutuwa wanda ya ƙunshi shawarwarin yadda gwamnati zata magance wahalhalin cire tallafin man fetur ga ma'aikata.

Haka zalika majalisar zata karɓi shawarwari da kuma tattauna batun mafi ƙarancin albashi da alawus-alawus ga ma'aikata don rage masu raɗadin halin da aka shiga.

Waɗanda suka halarci taron

Jiga-jigan da suka halarci taron sun haɗa da sakataren gwamnati, George Akume, shugaban NNPCL, Mele Kyari, muƙaddashin shugaban CBN, Folashodun Shonubi da muƙaddashin Akanta Janar na ƙasa.

Haka zalika manyan sakatarorin ma'aikatun albarkatun man fetur, noma, kasafi da tsare-tsaren ƙasa duk sun hallara a wurin wannan taro, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tsohon Shugaban Kasa Buhari Ya Kai Ziyarar Ta'aziyya Gidan Fitaccen Attajirin Ɗan Kasuwa

Shugaban ƙungiyar gwamnonin Najeriya kuma gwamnan Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq da shugaban gwamnonin APC, Hope Uzodinma, sun halarta.

Bugu da ƙari gwamnonin jihohin Gombe, Katsina, Lagos, Nasarawa, Ogun, Kaduna, Kebbi, Yobe, Delta, Bayelsa, Abia, Zamfara, Anambra, Bauchi, Jigawa, Cross River, Plateau, Edo, Benue, Akwa Ibom, da Sokoto suna wurin.

Amma gwamnonin jihohin Enugu, Oyo, Rivers, Adamawa, da Kano sun tura mataimakansu su wakilce su a wurin zaman NEC na yau Alhamis.

APC Na Duba Yuwuwar Maye Gurbin Adamu da Ganduje a Matsayin Shugaba

Rahoto ya nuna Ga dukkan alamu shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya fi natsuwa tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje ya maye gurbin shugaban APC.

Sakamakon haka har an cire sunan Ganduje daga cikin jerin sunayem Ministocin da shugaban ƙasa Tinubu ke dab da miƙa wa majalisar tarayya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262