Sojoji Sun Ragargaji Yan Ta’adda Ta Sama, Sun Kashe Mayaka 22 Masu Biyayya Ga Marigayi Abdulkareem Boss
- Dakarun rundunar sojin sama sun yi gagarumin nasara a kan yan ta'adda a yankin Batsari da Jibia da ke jihar Katsina
- Sojoji sun murkushe mayakan kungiyar ta'addanci 22 masu biyayya ga madugun dan ta'adda, marigayi Alhaji Abdulkareen Lawal wanda aka fi sani da Abdulkareen Boss
- Kakakin NAF, Air Commodore Edward Gabkwet, ya tabbatar da kai hare-haren
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Dakarun sojojin sama na Operation Hadarin Daji (OPHD) sun ragargaji yan ta'adda masu biyayya ga kasurgumin dan ta'adda, Alhaji Abdulkareen Lawal wanda aka fi sani da Abdulkareen Boss, a ranar Litinin, 17 ga watan Yuli.
Sojojin sun kashe mayakan ta'addanci 22 a yayin farmakin da suka kai a Batsari da Sola Poi II da ke kananan hukumomin Batsari da Jibia na jihar Katsina, Zagazola Makama ya rahoto.
An kaddamar da hare-haren ne bayan samun bayanan sirri da suka nuna cewa yan ta'addan ne suka aiwatar da sace-sacen mutane da hare-haren ta'addanci a wasu garuruwa da ke karamar hukumar Kankara ta jihar Katsina.
A cikin haka, bayanan sirri a SOLA POI II ya gano dumbin yan ta'adda da ke boye a wajen da nufin yin garkuwa tare da kaiwa matafiya hari a hanyar Jibia-Katsina.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Daga bisani, dakarun sojin sama na OPHD sun gudanar da wani aiki ta sama inda suka kashe 'yan ta'adda da dama tare da lalata gine-gine da maboyarsu.
Yadda dakarun sojoji suka murkushe Abdulkareem Boss a 2022
A tuna cewa hare-haren rundunar NAF na ranar 6 ga watan Agustan 2022 ya murkushe madugun dan ta'adda Alhaji Abdulkareem Lawal da wasu mayakansa a dajin Ruga da ke jihar Katsina.
Marigayi Abdulkareem Boss shine ya aiwatar da kisan kwamandan yan sanda na Dutsin Ma a ranar 5 ga watan Yulin 2022.
Wata majiya ta bayyana cewa bayan shafe tsawon kwanaki suna tsare-tsare da shirya yadda abubuwa za su kasance, dakarun OPHD sun yi barin wuta ta sama a kan sansanin Abdulkareem da mabuyarsa da ke dajin Rugu na jihar Katsina, wanda ya kai ga murkushe shi.
Rundunar sojin sama ta tabbatar da kai harin
Da aka tuntube shi, kakakin NAF, Air Commodore Edward Gabkwet, ya tabbatar da harin amma ya ki yin karin bayani kan lamarin.
Sai dai kuma ya bayyana cewa tun bayan da hau kujerar shugabanci, babban hafsan sojin sama, Air Vice Marshal Hasan Abubakar, ya umurci dukkanin kwamandojin da su hada hannu da sauran hukumomin tsaro a kokarinsu na kakkabe yan ta'adda da mabuyarsu.
Yan sanda sun kama masu garkuwa da mutane, sun kwato makamai
A wani labari na daban, rundunar yan sandan jihar Bauchi ta yi nasarar kama wasu da ake zaton masu garkuwa da mutane ne su bakwai sannan ta kwato makamai guda hudu a karamar hukumar Alkaleri da ke jihar.
Jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sandan jihar, SP Ahmed Wakil, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar.
Asali: Legit.ng