Tsadar Mai: Na Kusa Da Tinubu Ya Gargadi 'Yan Najeriya Kan Sukar Shugaban Kasa
- Bayo Onanuga wanda ya yi wa Shugaba Tinubu kakakin yaƙin neman zaɓe, ya nemi alfarmar ƴan Najeriya
- Onanuga ya buƙaci ƴan Najeriya su kai zuciya nesa su jira zuwan tallafin da Shugaba Tinubu ya yi alƙawari domin rage raɗaɗin da ake sha
- Na kusa da shugaban ƙasar ya kuma ja kunnen ƴan Najeriya kan sukar gwamnatin Tinubu a dalilin cire tallafin man fetur
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT, Abuja - Mai magana da yawun bakin Shugaba Tinubu a lokacin yaƙin neman zaɓe, Bayo Onanuga, ya buƙaci ƴan Najeriya da su ƙara haƙuri a yayin da ake ci gaba da jin raɗaɗin cire tallafin man fetur.
Jaridar Daily Trust tace a wani rubutu da ya yi a shafinsa na Twitter ranar Laraba da daddare, Onanuga ya yi gargaɗi kan sukar gwamnatin Tinubu a dalilin tashin gwauron zaɓi da farashin man fetur ya yi.
Ya yi nuni kan buƙatar yin haƙuri da fahimtar gwamnati, yayin da gaba ɗaya ƙasa ake ci gaba da jin raɗaɗin ƙari kudin man fetur.
Tallafin da Tinubu ya yi alƙawari na nan tafe, Onanuga
Onanuga ya buƙaci ƴan Najeriya da su jira tallafin da gwamnatin tarayya ta yi alƙawari, inda ya nuna ƙwarin gwiwarsa kan cewa waɗannan matakan za su taimaka wajen rage raɗaɗin da tashin kuɗin man fetur ɗin ya haifar.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ya yi nuni da alfanun da za a samu daga cire kuɗin da aka kashewa wajen tallafin man fetur ɗin, inda ya ce jihohi za su samu ƙarin ƙuɗaɗe domin gudanar da ayyukan ci gaban al'umma.
A kalamansa:
"A wannan lokacin na tashin kuɗin man fetur, ina son na yi roƙo ga mutanenmu da su ƙara haƙuri. A tare duk mu ke jin raɗaɗin. Duk waɗannan caccakar da ake yi wa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, a dakatar da su."
Jiki Magayi: Jam'iyyar Peter Obi Ta Yi Wa 'Yan Najeriya Shagube Kan Farashin Man Fetur, Ta Fadi Abinda Zai Faru Gaba
"Mu jira tallafin da gwamnatinsa ta yi alƙawari. Mu jira tallafin da za su ƙwararo daga kowace jiha yayin da aka turo musu ƙarin kuɗaɗe daga cikin kuɗin da aka tara na dai na biyan tallafin man fetur."
"Ba zai yiwu mu koma muna yabon tsarin tallafin man fetur ba inda mu ke kashe kuɗi sosai kan fetur a maimakon kan hanyoyi, ilmi da lafiya."
Shirye-Shiryen Rabon Tallafi Sun Kusa Kammala
A wani labarin kuma, shugaban ƙasa mai girma Bola Ahmed Tinubu, ya gana da mataimakinsa, Kashim Shettima, shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, da wasu gwamnonin APC kan rabon tallafi.
Ganawar shugabannin an yi ta ne domin kammala shirye-shiryen rabon tallafi ga ƴan Najeriya domin rage raɗaɗin da ake ciki a dalilin cire tallafin man fetur.
Asali: Legit.ng