Kamfanin Simintin Dangote Ya Siya Hannun Jari 168m a Wani Sabon Shiri
- Kamfanin simintin Aliko Dangote ya gudanar da shirin sake siyan hannun jarin da siyar a baya ga masu zuba hannun jari
- Shirin zai ba kamfanin damar samun hannun jari 128m a kasuwa ko a hannun masu zuba hannun jari da suka siya
- Shirin dai na sake siyan hannun jarin ana yinsa ne domin ƙara ƙarfafa hannun jarin kamfanin da ɗaga darajarsa
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Kamfanin simintin Dangote ya kammala shirin sake siyan hannun jarin shi na kwana biyu. Shirin ya haɗa da siyan hannun jari 168,735,593, wanda hakan yake zama matsayin kaso 1% na hannun jarin da aka sanya a kamfanin.
Shirin sake siyan hannun jarin an fara shi ne a ranar Litinin, 17 ga watan Yulin 2023, inda aka shirya kammalawa a cikin kwana biyu ko har sai an samu adadin yawan da ake son samu, sanarwar da kamfanin ya fitar ta tabbatar.
Idan ba a manta ba dai a cikin ƴan kwanakin nan kamfanin ya ƙaddamar da wani shirin aiki da fasaha domin magance matsalar gurɓacewar yanayi a dalilin hayaƙin da ya ke fita a masana'antar Obasajana da sauran masana'antun da ke aiki.
Shirin sake siyan hannun jari na kamfanin simintin Dangote
Kamfanin simintin na Dangote ya zaɓi ya sake siyan hannun jarin domin ƙara ƙarfin ikonsa da ƙara wa masu zuba hannun jari ƙwarin gwiwa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ta hanyar sake siyan hannun jarin, kamfanin ya rage yawan kadarorinsa, wanda hakan zai sanya ya ƙara samun tagomashi idan aka kwatanta da ƙin sake siyan hannun jarin.
Haka kuma, rage yawan hannun jarin zai bayar da damar ƙarin abinda za a samu a kan kowane hannun jari saboda ƙarin kuɗin shiga da tsabar kuɗi ƙwarara.
Arzikin Dangote Da Wasu Attajirai Ya Ragu
A wani labarin kuma, kun ji cewa hamshaƙin attajirin na nahiyar Afirika, Aliko Dangote, ya ɗan tafka asara tare da wasu manyan attarai a ƙasar nan.
Dangote, Abdulsamad Rabiu da Mike Adenuga sun samu karayar arziƙi har ta N423bn a cikin sa'o'i 2: kacal, a wata sabuwar kiɗiddiga da mujallar Forbes ta fitar.
Daga cikin attajiran uku, Abdulsamad Rabiu shi ne wanda arziƙinsa ya fi raguwa sosai inda ya rasa N267.8bn.
Asali: Legit.ng