Kamfanin Emadeb Ya Karya Ƙwarin NNPC Yayin Da Ya Shigo Da Litar Man Fetur Miliyan 27 Najeriya
- Wani kamfanin 'yan kasuwa mai zaman kansa, ya zama na farko da ya fara shigowa da man fetur Najeriya
- Shekaru aru-aru, kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC) ne kaɗai ke shigo da duk man da ake amfani da shi
- Tun bayan cire tallafin man fetur, hukumar da ke kula da harkokin man fetur wato NMDPRA, ta rabawa mutane da dama lasisin shigowa da mai Najeriya
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Legas - Daɗaɗɗen tsarin da ya bai wa kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC), shi kaɗai damar shigowa da mai Najeriya ya wargaje.
Wani kamfanin jigilar man fetur mai suna 'Emadeb Energy Services Limited' ne ya karya wannan ƙwarin na NNPC kamar yadda The Punch ta ruwaito.
A ranar Laraba, 19 ga watan Yuli ne kamfanin ya shigo da litar man fetur miliyan 27 zuwa Najeriya daga waje.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ko hakan na nufin man fetur zai yi sauƙi? Bayani dalla-dalla
Duk da ya kamata a ce samuwar ƙarin masu shigo da man fetur zai sauƙaƙa farashinsa, sai dai alamu sun nuna hakan ba mai yiwuwa ba ne.
Karyewar darajar da naira ke yi na taka muhimmiyar rawa wajen ƙara yawan kuɗaɗen da ake kashewa wajen shigo da man daga waje.
A yanzu haka ana kashe aƙalla dala 80 wajen shigo da duk gangar man guda ɗaya daga waje.
Shugaban kamfanin na 'Emadeb Energy' ya bayyana cewa, sai da kamfaninsa tare da haɗin gwiwar wasu bankuna biyar suka biya dala miliyan 17 domin ɗauko man nasu daga Togo zuwa Najeriya.
Kamfanin ya ce harkar ba me ɓullewa ba ce
Shugaban kamfanin na Emadeb Energy' Adebowele Olujimi, a yayin da yake karɓar man da ya iso daga waje, ya bayyana cewa harkar shigo da man fetur a yanzu ba mai ɓullewa ba ce.
Ya ce dole ne Gwamnatin Tarayya ta yi ƙoƙarin bin duk hanyoyin da suka kamata wajen gyara matatun man Najeriya.
Ya ce harkar tana buƙatar dalolin Amurka masu tarin yawa wajen tafiyar da ita, a dalilin haka ne yake ganin cewa harkar ba mai yiwuwa ba ce.
An wallafa hotunan yadda aka tarbi zango na farko na man fetur ɗin da kamfanin na 'Emadeb Energy' ya shigo da shi a shafin NMDPRA na Twitter.
Majalisa Wakilai ta ƙi amincewa da ƙudurin rage farashin man fetur
Legit.ng a baya ta kawo muku rahoto da ke cewa, Majalisar Wakilan Najeriya ta yi watsi da kudirin rage farashin man fetur da aka kawo gabanta.
Majalisar ta ce za ta kafa kwamitin da zai duba dalilin da ya sa aka samu ƙarin farashin man da kuma na ababen hawa a faɗin ƙasar.
Asali: Legit.ng