Wani Mutum Na Shirin Auren Surukarsa Bayan Mutuwar Matarsa

Wani Mutum Na Shirin Auren Surukarsa Bayan Mutuwar Matarsa

  • Wani mutum ya nemi surukarsa mai shekaru 57 ta aure shi bayan matarsa ta mutu tana da shekaru 34
  • Mutumin mai shekaru 46 ya rasa matarsa bayan ta haifa masa yara uku kuma a yanzu yana shirin sake aure
  • Ya ce baya son kawo wata daga waje cikin gidansa, amma wasu na kallon shirinsa na auren uwar matarsa a matsayin haramun

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wani magidanci na neman auren surukarsa (uwar matarsa) shekaru biyu bayan mutuwar matarsa.

A labarin da Azuka Onwuka ya wallafa a Facebook, mutumin ya ce gwanda ya auri mahaifiyar matarsa sannan ya guji kawo wata daga waje.

Magidanci na neman auren uwar matarsa
Wani Mutum Na Shirin Auren Surukarsa Bayan Mutuwar Matarsa Hoto: Getty Images/Jeffbergen and MoMo Productions.
Asali: Getty Images

Matar mutumin ta mutu tana da shekaru 34, inda ta bar yara uku, maza biyu da mace daya.

Mutumin wanda yanzu shekarunsa 46 yana neman auren mahaifiyar matarsa wacce ke da shekaru 57 a duniya.

Kara karanta wannan

Yan Sanda Sun Tsare Wani Matashi Dan Kwaya Da Ake Zargin Ya Shake Wuyan Mahaifiyarsa Har Lahira

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yayin da neman auren ya haddasa cece-kuce, mutumin ya dace cewa shine abun da yake so.

Karanta labarin:

"Wani mutum (an boye sunansa) ya rasa matarsa bayan sun haifi yara uku (maza biyu da mace daya). Matarsa ta mutu tana da shekaru 34 a duniya. Shekaru biyu bayan nan, yana son auren uwar matarsa mai shekaru 57 kuma bazawara. Shekarunsa 46. Ya ce baya son karin yara ko auren wata daga waje wacce za ta iya raba shi, ko muzguna wa yaransa. Wasu dangin iyalin biyu sun goyi bayan shawarar yayin da wasu ke adawa da hakan."

Jama'a sun yi martani

Uchechukwu Damian Ononachi:

"Baya bukatar auren uwar matar, sai dai idon daman suna soyayya. Abun da yake bukata shine neman matar ta dawo zama da su sannan ta kula da yaransa. Auren surukar ba daidai bane."

Kara karanta wannan

“Na Kadu”: Matashi Dan Shekaru 31 Ya Gano Ainahin Shekarun Amaryarsa Mako 2 Kafin Bikinsu

Chike Nnanyelu Bunch:

"A binciki su biyun da kyau a kan mutuwar matar."

Uzo Goodluck:

"Yanzu ina zargin surukar a kan mutuwar matarsa."

Ifeanyi Ugwu:

"Hakan haramun ne a al'adata."

Matashi ya gano shekarun amaryarsa na gaskiya makonni 2 kafin bikinsu

A wani labarin, mun ji cewa wani matashi dan shekaru 31 ya gano ainahin shekarun mai shirin zama amaryarsa kwanaki 14 kafin bikinsu.

A cewar wani mai suna Danky wanda ya wallafa labarin a Twitter, matashiyar ta bayyana cewa shekarunta 30 kuma duk suna son junansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng