“Ba Za Ki Iya Satar Amsa a Jarrabawa Ba”: Dalibar Jami’a Ta Gano Ita Kadai Ce a Ajinta

“Ba Za Ki Iya Satar Amsa a Jarrabawa Ba”: Dalibar Jami’a Ta Gano Ita Kadai Ce a Ajinta

  • Wani bidiyon TikTok ya nuno dalibar Najeriya wacce ita kadai ce a ajinta, kuma ta ce tana matukar son hakan
  • Matashiyar, Bumblebee ta wallafa bidiyon tana mai fada ma mutane yadda abun yake ace mutum yana karatu shi kadai ba tare da abokan karatu ba
  • Bumblebee tana karantar 'Petroleum Chemistry' a jami'ar Baze, Abuja kuma ta ce tana son bangaren da take karanta

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wata daliba da ke karantan fannin 'Petroleum Chemistry' a jami'ar Baze, Abuja ta ce ita kadai ce a ajinta.

Dalibar, Bumblebee ta wallafa wani bidiyo a shafinta na TikTok tana mai yi wa mabiyanta bayanin yadda ake ji ace mutum yana aji shi kadai.

Ita kadai ce a ajinta
“Ba Za Ki Iya Satar Amsa a Jarrabawa Ba”: Dalibar Jami’a Ta Gano Ita Kadai Ce a Ajinta Hoto: TikTok/@xoxoshaya.
Asali: TikTok

Bumblebee ta ce tana son bangaren abun da take karanta duk da cewar yana da matukar wahala sosai.

Kara karanta wannan

An Yi Son Kai: Majalisa Za Ta Binciki Duka Mukaman da Aka Bada a Mulkin Buhari

Yanzu haka tana aji hudu a jami'a amma ta ce akwai wasu dalibai uku a sauran ajujuwan, inda suka zama su hudu a gaba daya bangaren.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yarinyar da ke karatu ita kadai ta ce tana farin ciki

Sabanin abun da mutane za su yi tunani, Bumblebee ta ce bata jin kadaici. Koda dai karatun na da wahala, ta yi bayanin cewa tana jin dadin kasancewa ita kadai.

Babban kalubalen, a cewarta malaman suna sa ran ta san komai sannan ta lashe dukkanin kwasa-kwasan tunda ita kadai ce.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@DiiTee yace:

"Ke kadai wakiliyar kwas din, shugabar sashin kuma daliba mafi kwazo. Na tayaki murna."

@El nino ta ce:

"Baaba ba zan iya ba faa....Jarrabawa ba zai yi sauki ba. Wa zan kwafa?"

@c.v commented:

"Wato ba zan iya kin zuwa aji ba wasu ranaku?"

Kara karanta wannan

“Bai Taba Cin Amanata Ba”: Budurwa Ta Ki Amsa Tayin Saurayin Da Suka Shafe Shekaru 8 Suna Soyayya, Ta Fadi Dalili

@Deji ya ce:

"Ba za ki iya bacci ba a aji."

@babablu ya tambaya:

"Kenan ba za ki iya satar amsa ba a jarrabawa?"

Mmesoma Ejikeme: Dalibar da ta kirkiri sakamakonta na UTME ta nemi yafiyar JAMB

A wani labarin, Legit.ng ta kawo a baya cewa dalibar nan mai shekaru 19 wacce hukumar shirya jarabawar shiga jami’a (JAMB) ta zarga da kirkirar sakamakon jarrabawarta na UTME, Mmesoma Ejikeme, ta ba hukumar hakuri a kan abun da ta aikata.

Mmesoma ta karanto wani wasika na ban hakuri a yayin zaman sauraron rahoton kwamitin bincike da majalisar wakilai ta kafa domin bincikar lamarin karkashin jagorancin Sada Soli.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng