Buhari Ya Yi Wa Daukacin Al’ummar Musulmi Murnar Shiga Sabuwar Shekara
- Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika sakon gaisuwarsa ga daukacin al’ummar Musulmi a fadin duniya
- Sarkin Musulmi ya alanta ranar Laraba, 19 ga watan Yuli a matsayin ranar 1 ga watan Muharram na shekarar 1445 bayan Hijirah
- Buhari ya yi kira ga Musulman duniya da suyi koyi da koyarwan Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi
Tsohon shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari, a ranar Laraba, 19 ga watan Yuli, ya taya daukaci al’ummar Musulman Najeriya da na duniya murnar shiga sabuwar shekarar Musulunci 1445 bayan Hijrah.
Sakon Buhari na kunshe ne a cikin wata sanarwa da tsohon kakakin tsohon shugaban kasar, Malam Garba Shehu, ya saki a daren Laraba.
Dukkanmu baki ne a gidan duniyan nan, Buhari ga al'ummar Musulmi
Tsohon shugaban kasar ya yi kira ga Musulmai a fadin duniya da su yi koyi da koyarwar Annabi Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da sahabbansa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ya kuma bukaci al’ummar Musulmi da su tuna cewa gaba dayanmu baki ne a gidan duniya. Ya kuma nemi a yi wa kasar addu’a sannan ya kalubalanci yan kasar da su huji yin abubuwa ko kalaman da ka iya tarwatsa hadin kan kasar.
Mallam Garba Shehu ya rubuta a shafinsa:
“Tsohon shugaban kasa Buhari na gaishe da Musulmai yayin da suke murnar shiga sabuwar shekarar Musulunci.
“Ayayin bikin sabuwar shekarar Musulunci 1445, tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari yana kira ga daukacin Musulmai a fadin kasar da ma fadin duniya da su yi koyi da koyarwar Annabi Muhammad (SAW) da sahabbansa, tare da jaddada muhimmancin tunatar da kai cewa dukkanmu masu hijira ne a duniyar nan.
"Muna kira da ayi wa kasar addu'a sannan gaba daya yan kasa da mu hada kai wajen aikata khairan sannan mu guji aikata abubuwa ko kalaman da za su tarwatsa hadin kan kasa."
Bikin sabuwar shekarar Musulunci: Gwamnan Zamfara ya ba da hutunn kwana daya
A wani labarin kuma, mun ji cewa gwamnatin jihar Zamfara ta sanar da ranar Laraba, 19 ga watan Yuli a matsayin ranar hutu, domin murnar shiga sabuwar shekarar musulunci ta 1445 bayan Hijirah.
Sanarwar na zuwa ne biyo bayan al'adar gwamnatin jihar ta bayyana ranar 1 ga watan Muharram na kowace shekara a matsayin ranar hutu a jihar.
Asali: Legit.ng