Gwamnan Nasarawa Ya Yi Ganawar Sirri Da Babban Hafsan Tsaro Na Kasa Kan Kwararar 'Yan Ta'adda a Jiharsa

Gwamnan Nasarawa Ya Yi Ganawar Sirri Da Babban Hafsan Tsaro Na Kasa Kan Kwararar 'Yan Ta'adda a Jiharsa

  • Gwamnan jihar Nasarawa Abdullahi Sule, ya koka kan kwararowar 'yan ta'adda daga wasu jihohin zuwa jiharsa
  • Ya bayyana hakan ne jim kaɗan bayan wata ganawar sirri da ya yi da babban hafsan tsaron Najeriya a Abuja
  • Sule ya ce akwai buƙatar jami'an tsaro su kare jihar Nasarawa daga duk wata barazanar tsaro saboda kusancinta da Abuja

Abuja - Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya gana da babban hafsan tsaron ƙasa, Manjo Janar Christopher Musa, kan kwararowar 'yan ta'adda da wasu masu aikata miyagun laifuka zuwa jiharsa.

Gwamnan ya koka kan kwararowar 'yan ta'adda zuwa jiharsa waɗanda suke tserewa luguden da jami'an tsaro ke musu a ƙaramar hukumar Mangu ta jihar Filato kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Gwamna A Sule ya nemi agajin babban hafsan tsaron Najeriya
Gwamnan jihar Nasarawa Abdullahi Sule ya nemi babban hafsan tsaron Najeriya ya kawowa jiaharsa ɗauki. Hoto: Adamu Yusuf Musa
Asali: Facebook

Sule ya nemi a ɗauki matakin gaggawa saboda kusancin Nasarawa da FCT

Kara karanta wannan

"Matata Tana Zabga Mun Mari Ta Lakaɗa Mun Duka Kamar Jaki" Ɗan Kasuwa Ya Nemi Saki a Kotu

Gwamnan ya kuma bayyana cewa jihar tasa na fuskantar yaɗuwar makamai sakamakon kwararowar 'yan ta'addan.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Da yake zantawa da manema labarai bayan ganawar a hedkwatar tsaron da ke Abuja, Abdullahi Sule ya ce ya zo ne don ya sanar da babban hafsan tsaron domin a ɗauki matakin gaggawa kan lamarin.

Ya ƙara da cewa hakan ya zamo dole musamman in aka yi duba da yadda jihar ke da kusanci da babban birnin tarayyar Najeriya.

Ya ce sun tattauna batutuwa da suka shafi tsaro, waɗanda yake da yaƙinin cewa za a ɗauki matakan da suka dace a kansu.

Sojoji na ɗaukar matakan da suka dace

Da yake hira da 'yan jarida bayan ganawa da gwamnan, Manjo Janar Musa ya ce jami'ansu sun gama shiri tsaf domin tunkarar ƙalubalen.

Ya ce abu ne mai muhimmanci a garesu su bai wa jihar Nasarawa tsaro, musamman saboda da kusancinta da babban birnin tarayyar Abuja.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Ɗumi: Gwamnan PDP Ya Kori Ma'aikata 1,700 Daga Aiki, Ya Umarci Su Dawo da Abinda Aka Ba Su

Ya ce a yanzu haka jami'ansu na ƙoƙarin ganin sun daƙile duk wata barazanar tsaro a jihar ta Nasarawa.

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa, tun a ranar Talata da ta gabata ne gwamnan ya fara kokawa kan kwararowar 'yan ta'addan da ya ce suna zuwa ne daga jihohin da ke maƙwabtaka da Nasarawa.

Yajin aikin likitoci ya janyo rasa ran mace mai juna biyu a Nasarawa

Legit.ng a baya ta kawo muku wani rahoto kan wata mata mai juna biyu da ta rasa ranta saboda rashin likitocin da za su kula da ita a jihar Nasarawa.

Hakan ya faru ne sakamakon wani yajin aiki na wucin gadi da likitocin jihar suka shiga don kai kokensu ga gwamnatin jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng