Gwamnatin Tarayya Za Ta Hana Masu POS Tsayar Da Sabon Farashi
- Gwamnatin Tarayya ta sha alwashin ɗaukar mataki mai tsauri kan masu sana'ar POS
- Gwamnatin ta ce a baya ta shawarci masu sana'ar ta POS dangane da ƙarin kuɗaɗen cajin da suke yi
- Ta bayyana hakan ne ta hannun mataimakin shugaban Hukumar Gasa Da Kare Haƙƙin Kwastomomi ta Tarayya Babatunde Irukera
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Gwamnatin Tarayya ta sha alwashin dakatar da masu sana'ar cire kuɗi wato POS, daga tashin farashin cajin da ake yi yayin cirar kuɗaɗe.
Gwamnatin ta bayyana hakan ne ta Hukumar Gasa Da Kare Hakkin Kwastomomi ta Tarayya (FCCPC).
Mataimakin shugaban Hukumar ta FCCPC, Babatunde Irukera ne ya bayyana hakan a zantawarsa da jaridar The Punch.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sun shawarci masu sana’ar ta POS da farko
Babatunde ya bayyana cewa a baya sun shawarci masu sana’ar dangane da batun, inda ya ce har yanzu ba su yi amfani da shawarar tasu ba.
Hakan ne a cewarsa ya sa hukumar zuwa da wasu sabbin matakan da za su tursasa duk masu sana’ar bin umarnin gwamnati.
Ya ce nan ba da jimawa ba umarni zai iso kan sabbin dokoki da za su yi aiki kan masu harkar ta POS da makamantansu.
FCCPC za ta ɗauki mataki mai tsauri kan kungiyoyin 'yan kasuwa
A wani rahoto da Legit.ng ta kawo a baya, Hukumar Gasa Da Kare Haƙƙin Kwastomomi ta bayyana cewa za ta ɗauki mummunan mataki kan kungiyoyin 'yan kasuwa.
Hukumar ta ce ɗaukar matakin ya zama wajibi duba da yadda ƙungiyoyin 'yan kasuwar ke ƙara farashi yadda suka dama kuma a kowane lokaci.
Ya ƙara da cewa matakin nasu zai taimaka wajen daƙile hauhawar farashin kayayyakin da ake samu tun bayan sanar da dokar ta ɓaci a kan abinci da Tinubu ya yi.
Majalisar Wakilai za ta binciki muƙaman da aka ba da lokacin Buhari
Legit.ng a baya ta kawo rahoto da ke cewa Majalisar Wakilan Najeriya za ta binciki duk wasu muƙaman da aka ba da a lokacin mulkin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.
Majalisar dai za ta gudanar da binciken ne sakamakon son kai da take zargin an yi yayin raba muƙaman.
Asali: Legit.ng