Muhammadu Buhari Ya Ziyarci Dahiru Mangal Bisa Rasuwar Matarsa

Muhammadu Buhari Ya Ziyarci Dahiru Mangal Bisa Rasuwar Matarsa

  • Tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya kai ziyarar ta'aziyya gidan ɗan kasuwan nan, Alhaji Ɗahiru Mangal
  • Buhari, tare da rakiyar gwamna Malam Dikko Raɗda ziyarci fadar mai martaba Sarkin Katsina, Abdulmumini Kabir Usman
  • Manyam jiga-jigai kamar gwamnoni da sauran masu faɗa a aji a ƙasar nan na ci gaba da tururuwar zuwa gidam Mangal ta'aziyyar rasuwar matarsa

Katsina state - Fitaccen attajirin ɗan kasuwan nan, Alhaji Ɗahiru Mangal, na ci gaba ta karban bakuncin manyan mutane a ƙasar nan da suke zuwa masa ta'aziyya bisa rasuwar matarsa.

A ranar Laraba, tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya bi sahun zuwa har gida yi wa iyalan Mangal ta'aziyyar rasuwar Hajiya Aisha Ɗahiru Mangal.

Buhari a gidam sarkin Katsina.
Muhammadu Buhari Ya Ziyarci Dahiru Mangal Bisa Rasuwar Matarsa Hoto: @Miqdad_jnr
Asali: Facebook

Hajiya Aisha ta rasu ne a wani Asibiti a babban birnin tarayya Abuja ranar Asabar da ta gabata bayan fama da jinya kuma tuni aka mata jana'iza ranar Lahadi a Katsina.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Gana da Tsohon Shugaban Ƙasa da Wasu Gwamnoni 3 a Villa, Bayanai Sun Fito

Gwamnan jihar, Malam Dikko Raɗda ne ya raka Buhari zuwa gidan Mangal domin yi masa ta'aziyyar wannan rashi, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka nan kuma tsohon hadimin shugaban ƙasa, Tunde Sabiu, na tare da Muhammadu Buhari a lokacin wannan ziyara.

Tsohon shugaban ƙasan ya yi Addu'ar Allah ya yi wa mamaciyar rahama kuma ya roƙi Allah SWT ya bai wa Mangal da sauran iyalansa haƙurin wannan rashi.

Buhari ya kai ziyara ga Sarkin Katsina

Haka zalika, Buhari tare da rakiyar gwamna Dikko Raɗɗa, ya ziyarci mai martaba Sarkin Katsina, Dakta Abdulmumini Kabir Usman, a fadarsa.

Bugu da ƙari, Buhari ya halarci taron gidauniyar Katsina 2023 wanda ya gudana a gidan gwamnatin jihar ranar Laraba.

Jiga-jigan suka je ta'aziyyar rasuwar matar Mangal

Sauran manyan mutanen da suna je ta'aziyyar rasuwar Hajiya Aisha Mangal sun haɗa da, Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf da gwamnan Zamfara, Dauda Lawal.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Aike da Muhimmin Saƙo Ga Ɗahiru Mangal da Fitaccen Malamin Musulunci a Najeriya

Wakilan ƙungiyar gwamnonin arewa karkashin jagorancin gwamnan Gombe, Inuwa Yahaya, na daga cikin waɗanda suka je ta'aziyya.

Mambobin Kwamitin Gudanarwa Na APC Zasu Gana da Gwamnoni a Abuja

A wani labarin na daban kuma Kwamitin gudanarwa na APC ta ƙasa (NWC) ya shirya zama da gwamnonin jam'iyya mai mulki yau Laraba a Abuja.

Wannan taro na zuwa ne awanni 48 kacal bayan mataimakin shugaban APC na shiyyar arewa, Abubakar Kyari, ya karbi ragamar jam'iyya a matsayin muƙaddashin shugaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262