Yanzu-Yanzu: Majalisar Wakilai Ta Yi Watsi Da Kudirin Rage Farashin Man Fetur
- Majalisar wakilai ta ƙi amincewa da ƙudirin neman ta dakatar da ƙarin farashin kuɗin man fetur da aka yi a ƙasar nan
- Majalisar ta ƙi amincewa da ƙudirin ne saboda a cewarta ta kafa kwamiti wanda zai yi bincike kan dalilin yin ƙarin
- Ƴan majalisun sun kuma kafa wani kwamiti na wucin gadi wanda zai samo hanyoyin rabon tallafi ga ƴan Najeriya
FCT, Abuja - Mambobin majalisar wakilai sun watsawa ƴan Najeriya ƙasa a ido kan kiraye-kirayen da ake yi na a dakatar da ƙarin farashin man fetur.
Ƴan majalisar wakilan dai sun yi watsi da kirayen-kirayen na dakatar da ƙara farashin kuɗin man fetur daga N537 zuwa N617 kan kowace lita ɗaya, rahoton Nigerian Tribune ya tabbatar.
Wannan dai zuwa ne kusan kwana shida bayan ƴan majalisun sun amince a basu tallafin N70bn daga cikin tallafin N500bn da aka shirya domin rage raɗaɗin cire tallafin farashin man fetur.
A zaman majalisar na ranar Laraba, 19 ga watan Yuli, majalisar ta yi watsi da ƙudirin dakatar da ƙarin farashin man fetur da komawa kan tsohon farashi na N537 kan kowace lita, rahoton The Nation ya tabbatar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A maimakon hakan, majalisar ta amince da kafa kwamitin da zai binciki dalilin ƙarin kuɗin man fetur da na kuɗin ababen hawa ba zato ba tsammani a faɗin ƙasar nan.
Majalisar ta kuma buƙaci kwamitin da ya samo hanyoyin bayar da tallafi da za a bi domin tsamo ƴan Najeriya daga cikin halin ƙuncin da su ke ciki.
Dalilin majalisar na ƙin dakatar da ƙarin farashin man fetur ɗin
Majalisar wakilan ta bayyana cewa tun da har ta riga da ta kafa kwamitin da zai yi bincike kan ƙarkn kuɗin, dakatar da ƙarin farashin kuɗin man fetur zai zama kamar ƙin barin kwamitin ya gudanar da aikinsa ne.
Jiki Magayi: Jam'iyyar Peter Obi Ta Yi Wa 'Yan Najeriya Shagube Kan Farashin Man Fetur, Ta Fadi Abinda Zai Faru Gaba
Sai dai, ƴan majalisar sun amince su kafa wani kwamiti na wucin gadi wanda zai ƙunshi kowane yanki daga cikin yankuna shida da ake da su a ƙasar nan domin rabon kayan tallafin ga ƴan Najeriya.
LP Ta Yi Wa 'Yan Najeriya Shagube
A wani labarin kuma, jam'iyyar Labour Party (LP) ta yi wa ƴan Najeriya shaguɓe kan ƙarin farashin kuɗin man fetur da aka yi a ƙasar nan.
Jam'iyyar ta bayyana cewa wannan somin taɓi ne cikin irin wuyar da ƴan Najeriya za su sha a ƙarƙashin mulkin Shugaba Bola Tinubu na jam'iyyar APC.
Asali: Legit.ng