Emefiele: Dakataccen Gwamnan CBN Ya Tunkari Kotu da Bukatar Beli

Emefiele: Dakataccen Gwamnan CBN Ya Tunkari Kotu da Bukatar Beli

  • Gwamnan babban banki CBN, Mista Godwin Emefiele, ya nemi babbar Kotun tarayya mai zama a Abuja ta bada belinsa
  • Mista Emefiele ta hannuna lauyansa, Joseph Daudu, ya faɗa wa Kotun zargin da ake masa yana da beli kuma bai taɓa aikata laifi ba
  • Har yanzu ba bu tabbacin ranar da hukumar DSS zata gurfanar da Emefiele a gaban Kotu

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Lagos - Dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya roƙi babbar Kotun tarayya mai zama a jihar Legas ta bada belinsa gabanin fara sauraron tuhumar da ake masa.

Channels tv ta rahoto cewa Emefiele ya buƙaci Kotun ta taimaka ta bada umarnin a sake shi a matsayin beli gabanin yanke hukunci a ƙarar da gwamnatin tarayya ta shigar.

Dakataccen gwamnan CBN, Mista Godwin Emefiele.
Emefiele: Dakataccen Gwamnan CBN Ya Tunkari Kotu da Bukatar Beli Hoto: channelstv
Asali: UGC

Emefiele ya gabatar da wannan buƙata a gaban Kotu ne ta hannun lauyoyinsa ƙaraƙashin babban lauya, Joseph Daudu (SAN).

Kara karanta wannan

Kano: Ganduje Ya Magantu Kan Batun Ciyo Bashin Biliyan 10 Don CCTV, Ya Fayyace Gaskiyar Al'amari

Yaushe Gwamnati zata fara gurfanar da Emefiele a gaban Kotu?

Har kawo yanzu ba bu tabbacin yaushe za a gurfanar da gwamnan CBN da aka dakatar a gaban Kotun kan tuhume-tuhume biyu, mallakar bindiga da alburusai ta haramtacciyar hanya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Amma alamu sun nuna za a gurfanar da shi ne a wani lokacin cikin hutun shekara-shekara da Kotu zata tafi wanda zai fara daga ranar 24 ga watan Yuli, 2023.

Rahoto ya nuna an damƙa Kes din dakataccen gwamnan CBN hannun mai shari'a Nicholas Oweibo, wanda yana ɗaya daga cikin alkalai 2 da suka tafi hutu, ɗayan shi ne mai shari'a Akintayo Aluko.

Emefiele ya kafa hujjoji 9 a buƙatar neman beli

Takardar buƙatar belin Mista Emefiele na kunshe da dalilai 9. Na ɗaya ya ce tuhumar da ake masa tana da beli. Haka nan ya ce ba a taɓa gurfanar da shi gaban Kotu ba.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Farmaki Har Cikin Fada, Sun Halaka Babban Sarki a Najeriya

Ya shaida wa Kotu ta hannun lauyansa cewa duk da a yanzu ana tuhumarsa kan wasu laifuka, har yanzu ba shi da laifi har sai an tabbatar da abinda ake zarginsa a kai, rahoton The Cable ya tattaro.

Gwamnan PDP Na Tsaka Mai Wuya a Gaban Kotu, INEC Ta Gaza Kare Zaben da Ya Ci a 2023

A wani labarin kuma Hukumar INEC ta gaza gabatar da shaidu domin kare kanta da tabbatar da nasarar gwamnan Enugu na PDP a zaben 2023.

Lauyan PDP , Benjamin Nwosu, da kuma lauyan gwamna.Mbah ba su yi musu da matakin INEC ba. Ana tsammanin PDP zata fara kare kanta nan ba da jima wa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262