Gwamnatin Rivers Ta Kori Ma'aika 1,700 a Jami'ar Jihar, Ta Basu Sabon Umarni
- Gwamnatin jihar Ribas karkashin gwamna Fubara ta kori ma'aikatan jami'a sama da 1,000 daga aiki bayan wata 6 da fara aiki
- Kwamishinan ilimi na jihar, Farfesa Prince Chinedu Mmom, ne ya tabbatar da haka a wata sanarwa da ya fitar
- Ya kuma umarci dukkan waɗanda matakin ya shafa su maida takardun ɗaukar aiki da ID Card ɗin da aka ba su
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Rivers state - Gwamnatin jihar Ribas karkashin gwamna Siminialaye Fubara ta bayyana cewa ta kori ma'aikata 1,700 da aka ɗauka aiki a jami'ar ilimi ta Ignatius Ajuru da ke Rumuolumeni.
Jaridar Vanguard ta tattaro gwamnatin na bayanin cewa ta sallami ma'aikatan jami'ar daga aike sakamakon gano cewa ba a bi ƙa'idoji da matakan doka wajen ɗaukarsu aikin ba.
Gwamnatin Ribas a zamanin mulkin Nyesom Wike ce ta ɗauki ma'aikatan na ɓangaren koyarwa da mara koyarwa a jami'ar.
Amma watanni kalilan bayan hawa kan mulki, gwamna Siminialaye Fubara ya sanar da soke ɗaukar sabbin ma'aikatan da magabacinsa ya yi a jami'ar.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Gwamna ya umarci su dawo da takardun da aka ba su
Gwamnatin Fubara ta kuma umarci kafatanin ma'aikatan da korar da shafa, waɗanda sun kai wata 6 suna aiki, su gaggauta maida takardan ɗaukan aikin da jami'a ta basu da katin shaida.
Kwamishinan ilimi na jihar Ribas, Farfesa Prince Chinedu Mmom, ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya rattaɓa wa hannu mai ɗauke da kwanan watan 13 ga Yuli.
Farfesa Mmom ya ce:
"Gwamnatin Ribas ta gano akwai kauce hanya da saɓa doka a aikin ɗaukar ma'aikatan da ba a jima da kammala wa ba a jami'ar Ignatius Ajuru da ke Rumuolumeni a Patakwal."
"Saboda haka ta soke ɗaukar aikin da hukumar jami'ar ta aiwatar kwanan nan. Duk takardun aikin da aka raba wa sabbin ma'aikatan an soke su kuma ana umartan a maida su ofishin rijistara."
"Sauran abubuwan da suka danganci ɗaukar aiki da aka raba wa sabbin ma'aikatan kamar katin shaida watau ID Card, ana umartan su hanzarta miƙa su ofishin shugaban ma'aikatan Ribas."
Gwamnatin Jihar Abiya Ta Musanta Korar Kwararrun Likitoci Daga Bakin Aiki
A wani labarin na daban kuma Gwamnatin jihar Abiya karƙashin gwamna Alex Otti ta ƙaryata raɗe- raɗin da ke yawo cewa ta kori baki ɗaya ma'aikatan lafiya daga aiki.
Kwamishinar lafiya, Dakta Ngozi Okoronkwo, ta ce rahoton ba shi da tushe balle makama domin ba bu wani abu makamancin haka a yanzu.
Asali: Legit.ng