NNPC Ya Bayyana Dalilin Tashin Farashin Mai A Kasar Zuwa N617

NNPC Ya Bayyana Dalilin Tashin Farashin Mai A Kasar Zuwa N617

  • Kamfanin mai na NNPC ya yi karin haske kan tashin farashin man fetur da aka fuskanta a yau
  • Shugaban kamfanin, Mele Kyari ya bayyana haka ne ga 'yan jaridu a yau Talata a Abuja
  • Ya ce tashin farashin ba shi da alaka da karancin man fetur, ya alakanta hakan da 'yan kasuwa

FCT, Abuja - Shugaban Kamfanin mai na NNPC, Mele Kyari ya bayyana dalilin tashin farashin mai a safiyar yau Talata 18 ga watan Yuli.

Kyari ya ce wannan tashin farashin ba shi da alaka da karancin man fetur a kasar kamar yadda ake yadawa.

NNPC Ya Bayyana Dalilin Tashin Farashin Mai A Kasar Zuwa N617
Shugaban Kamfanin Man Fetur, NNPC Ya Yi Bayanin Kan Dalilin Tashin Farashin Mai A Kasar. Hoto: NNPC.
Asali: Facebook

Ya ce tashin farashin man fetur din na da alaka da sauyin farashi daga 'yan kasuwa, Punch ta tattaro.

NNPP ya bayyana dalilin tashin farashin man fetur

Kyari ya bayyana haka ga 'yan jaridu bayan wata ganawar sirri da mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima a Abuja, TheCable ta tattaro.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Sabuwar Matsala Ta Ɓullo a Abuja da Kano Bayan Tashin Farashin Mai Zuwa N620

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ce karin farashin daga 'yan kasuwa ne kuma ya na iya yin sama ko kasa.

Ya ce:

"Wannan farashi ya danganci 'yan kasuwa ne, wannan shi ne ma'anar 'yan kasuwa su rinka gudanar da farashin.
"Farashin zai na sauyawa, wata rana ya yi sama wata rana kuma ya yi kasa."

Wannan na zuwa ne bayan farashin man fetur ya tashi daga N540 a kan lita zuwa N617 a safiyar yau Talata 18 ga watan Yuli, cewar THISDAY.

Ya karyata rade-radin da ake cewa wai hakan na da nasaba da karancin mai din a kasar.

Ya ce akwai tulin mai a kasar kuma wadatacce

Ya tabbatar da cewa:

"Wannan sauyin farashin ba shi da alaka da yawan mai da ake batarwa, ba wannan ne matsalar ba.
"Idan ka je kasuwa ka sayi kaya, za ka siyar a kasuwa yadda farashin wurin ya kama, babu batun cewa karancin mai ne ya jawo, ba mu da wannar matsalar.

Kara karanta wannan

Renewed Hope ko Wahala: An fara dawowa daga rakiyar Tinubu kan tashin kudin fetur

"Muna da wadataccen mai a kasa, mun samar da mai har ma tsawon kwanaki 32, wannan ba matsala ba ne."

A bangarensa, shugaban hukumar NMDPRA, Faroul Ahmed ya alakanta tashin farashin mai din da tsadar danyen mai a duniya.

Ya kara da cewa yawan kashe-kashen kudade yayin shigo da man a bangaren dillalan man fetur shi ma na daga cikin dalilan.

FG Ta Magantu Kan Karyewar Farashin Mai Bayan Dillalan Man Sun Fara Shigo Da Shi Kasar

A wani labarin, Hukumar Kula da Albarkatun Man Fetur (NMDPRA) ta bayyana cewa dillalan man fetur sun fara shigo da shi kasar.

Hukumar ta bayyana haka ne ta bakin shugabanta, Faroul Ahmed inda ya ce hakan zai rage farashin man.

Ya ce kamfanoni 56 ne ke neman lasisin shigo da man, inda ya ce uku daga ciki sun fara shigo da shi kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.