Gwamnatin Jihar Abiya Ta Musanta Korar Kwararrun Likitoci Daga Bakin Aiki

Gwamnatin Jihar Abiya Ta Musanta Korar Kwararrun Likitoci Daga Bakin Aiki

  • Gwamnatin jihar Abiya karƙashin gwamna Alex Otti ta ƙaryata raɗe-raɗin da ke yawo cewa ta kori baki ɗaya ma'aikatan lafiya daga aiki
  • Kwamishinar lafiya, Dakta Ngozi Okoronkwo, ta ce rahoton ba shi da tushe balle makama domin ba bu wani abu makamancin haka a yanzu
  • Ta yi kira ga ɗaukacin al'umma su yi fatali da jita-jitar kana su mara wa yunkurin gwamnati baya domin inganta ɓangaren lafiya

Abia state - Gwamnatin jihar Abiya karkashin shugabancin gwamna Alex Otti ta musanta raɗe-raɗin cewa gwamna ya kori baki ɗaya kwararrun likitoci da sauran ma'aikatan lafiya daga aiki.

Kwamishinar lafiya ta jihar Abiya, Dakta Ngozi Okoronkwo, ta musanta rahoton wanda ta kira da labarin kanzon kurege, mara tushe ballantana makama.

Gwamna Alex Otti na jihar Abiya.
Gwamnatin Jihar Abiya Ta Musanta Korar Kwararrun Likitoci Daga Bakin Aiki Hoto: channelstv
Asali: UGC

Channels tv ta tattaro cewa, Dakta Ngozi ta ce ko kaɗan gwamnatin Abiya ba ta kori kwararrun likitoci da sauran ma'aikatan lafiya ba.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Farmaki Har Cikin Fada, Sun Halaka Babban Sarki a Najeriya

Kwamishinar ta ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Rahoton korar baki ɗaya ma'aikatan lafiya tunanin banza ne na gurɓatattun mutanen da suka kirkiro labarin domin gwamnati ba ta da niyyar korar likita ko jami'an lafiya daga aiki."
"Ma'aikatan da muke da su yanzu, su mu ke tsammanin zasu taimaka a kokarin mu na kawo gyara da garambawul a ɓangaren lafiya na jihar Abiya."

Shin dagaske gwamnatin Abiya zata ɗauki ma'aikatan lafiya?

Bugu da ƙari, kwamishinar ta kuma jaddada cewa ba bu wani ma'aikacin lafiya da aka umarci, "Ya sake rubuta takardar neman ɗaukarsa aiki," inda ta ayyana labarin da ake yaɗa wa da tsagwaron ƙarya.

Dakta Ngozi ta shawarci kwararrun likitoci da malaman lafiya da sauran ɗaukacin al'ummar jihar Abiya da su yi watsi da jita-jitar da ake yaɗa wa.

Ta kuma buƙaci su mara wa yunkurin gwamnati baya yayin da take kokarin inganta ɓangaren kiwon lafiya domin kyautata rayuwar talakawa, kamar yadda Tribune ta rahoto.

Kara karanta wannan

Asiri Ya Tonu: Sabon Gwaman Ya Bankaɗo Ma'aikatan Bogi Sama da 2,000, Ya Tara Kuɗi N200m

Farashin Litar Man Fetur Ya Kara Tashi Zuwa N617 a Najeriya

A wani rahoton kuma 'yan Najeriya sun wayi gari da tashin farashin man Fetur a birnin Abuja da wasu sassan ƙasar.

Farashin litar man fetur ta ƙara tashi daga N539 zuwa sama da N600 a tsakiyar birnin tarayya Abuja da safiyar Talata, 18 ga watan Yuli, 2023.

A wata ziyara domin tabbatarwa da aka kai gidan man NPPC a Abuja, an gano cewa kamfamin mai na kasa ya ƙara farashi zuwa N617.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262