“Allah Ne Ya Cece Ni Fa”: Dirama Yayin da Matashi Ya Gano Ainahin Shekarun Amaryarsa Kwanaki 14 Kafin Biki

“Allah Ne Ya Cece Ni Fa”: Dirama Yayin da Matashi Ya Gano Ainahin Shekarun Amaryarsa Kwanaki 14 Kafin Biki

  • Soyayyar wasu masoya ya shiga halin rashin tabbass bayan mutumin ya gano ainahin shekarun mai shirin zama amaryar tasa
  • Masoyan sun fada tarkon son junansu har zuwa lokacin da mutumin mai shekaru 31 ya gano ta yi masa karyan shekarunta makonni biyu kafin bikinsu
  • Labarin ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya yayin da wasu suka ba mutamin shawarar ya janye daga lamarin

Wani matashi dan shekaru 31 ya gano ainahin shekarun mai shirin zama amaryarsa kwanaki 14 kafin bikinsu.

A cewar wani mai suna Danky wanda ya wallafa labarin a Twitter, matashiyar ta bayyana cewa shekarunta 30 kuma duk suna son junansu.

Hoton budurwa da wani matashi
“Allah Ne Ya Cece Ni Fa”: Dirama Yayin da Matashi Ya Gano Ainahin Shekarun Amaryarsa Kwanaki 14 Kafin Biki Hoto: Westend61
Asali: Getty Images

Yan kwanaki kafin aurensu, ya gano cewa shekarunta 37. Danky ya tambayi mutane kan irin matakin da za su dauka idan ace sune mutumin. Ya rubuta.

Kara karanta wannan

“Bai Taba Cin Amanata Ba”: Budurwa Ta Ki Amsa Tayin Saurayin Da Suka Shafe Shekaru 8 Suna Soyayya, Ta Fadi Dalili

"Shekarunsa 31, ita kuma 30 sannan su dukka suna son junansa. Makonni biyu kafin auren, ya gano cewa shekarunta 37, me za ka yi?"

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu mutane sun shawarci mutumin da ya janye, yayin da wasu suka bukaci ya yafewa matar sannan ya ci gaba da shirye-shiryen bikin.

Kalli rubutun Danky a kasa:

Jama'a sun yi martani

@thatEdochick ya ce:

"Me yasa yake zagaye-zagaye da duba ko'ina yanzu ya ga abun da bai kamata ya gani ko ya sani ba...ya ci gaba da shirin aurenta don Allah wannan karamin karya ne don Allah."

@farmacopoeia ya ce:

"Soyayya na yafiya. Tana da dalilanta na boye irin wannan bayani kuma idan har ba zai yi illa ko rusa wani ba, toh ya kamata ya ci gaba da shirin auren amma da wata daban.

@mister_ade5 ya ce:

"Baaba, Zan hakura da auren ne faa. ni da nake ganiyar kuruciya yanzu, za ki lalata mun da tsufanki."

Kara karanta wannan

Yanzu nan: Shugaban APC Ya Hakura da Rikon Jam’iyya, Ya Sauka Daga Kujerarsa

@konyeik ya ce:

"Duk soyayyar da aka gina ta kan karya ba zai yi karko ba. Wa ya san menene gaskiya ko karya daga gareta ba."

Budurwa ta ki amsa tayin saurayinta da suka shafe shekaru 8 tare, ta fadi dalili

A wani labarin kuma, wata matashiyar budurwa ta ki amsa tayin auren saurayinta bayan sun shafe tsawon shekaru takwas suna shan soyayya.

Matashiyar dai ta ki yarda da bukatar nasa ne saboda ba shi da kwakkwaran sana'ar da zai iya kula da ita da dansu guda daya da suka haifa tare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng