Mai Martaba Sarki Ya Nada Sabon Mai Zaben Sarki a Masarautar Gombe

Mai Martaba Sarki Ya Nada Sabon Mai Zaben Sarki a Masarautar Gombe

  • Sarkin Gombe Alhaji Abubakar Shehu Abubakar III, ya nada Alhaji Ahmad Abubakar Walama a matsayin sabon Sarkin Malaman Gombe
  • A yanzu Abubakar Walama ya kuma zama daya daga cikin masu nada sarki takwas na majalisar masarautar
  • Sarkin Malaman ya sha alwashin hada kan shugabannin addinai da wanzar da zaman lafiya a tsakanin mabiya addinai da kabilun jihar

Gombe - Mai martaba sarkin Gombe, Alhaji Abubakar Shehu Abubakar III, ya nada Alhaji Ahmad Abubakar Walama a matsayin sabon Sarkin Malaman Gombe’ kuma daya daga cikin masu nada sarki takwas a majalisar masarautar, Daily Trust ta rahoto.

Da yake gabatarwa Walama da wasikar nadin nasa, Shamakin Gombe, Alhaji Usman Muhammad, ya ce bayan tattaunawa da dama, Sarki Abubakar III, ya nada shi saboda ya tabbatar da cewar ya cancanta kuma ya dace da matsayin.

Kara karanta wannan

An Damke Sarkin Arewa da Mai Dakinsa a Kudancin Najeriya Saboda Alaka da Emefiele

Mai martaba Sarkin Gombe
Sarkin Gombe Ya Nada Sabon Mai Zaben Sarki a Masarautarsa. Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Walama ya gaji babban yayansa mai rasuwa, Muhammad Wabili Abubakar, wanda shine Sarkin Malamai ba biyu, shugaban malaman majalisar masarautar Gombe, wanda ya rasu a watan Disambar 2019.

Shamakin Gombe ya bukace shi da ya mutunta ka’idoji da al’adu da dabi’un wannan masarauta sannan ya yi amfani da mukaminsa wajen hada kan dukkanin malaman Musulunci don ci gaban masarautar da jihar.

Sabon sarkin malaman Gombe ya yi jawabin godiya

Da yake jawabin godiya, Walama, wanda ya kasance tsohon kwamishinan kananan hukumomi da harkokin masarautu, kuma shugaban karamar hukumar Dukku ta jihar sau biyu ya bayar da tabbacin cewa nadin nasa zai sabonta muradin mutane na samun zaman lafiya a tsakanin addinai da kabilu da ke zaune a fadin jihar.

A cewarsa, a matsayinsa na daya daga cikin masu nada sarakunan masarautar Gombe zai wakilta sannan ya shiga takanin kungiyoyin addinai domin tabbatar da wanzuwar zaman lafiya da ci gaba a jihar.

Kara karanta wannan

Gwamna Inuwa Yahaya Ya Rantsar Da Farfesa Njodi a Matsayin SSG, Ya Kaddamar Da Kwamitin Masu Ba Shi Shawara

Walama ya ce:

"Zan yi amfani da mukamina wajen samar da hadin kai tsakanin malamai da kuma wanzar da zaman lafiya da aminci a tsakanin daukacin mabiya addinai da suka hada da Musulmai da Kiristoci. Ya zama dole mu zauna lafiya saboda al'ummarmu ta samu ci gaba. Wannan zai zama babban abun da zan sanya a gaba yayin da na dauki wannan matsayin a masarautar.
"Na yi aiki a matsayin shugaban karamar hukumar Dukku na shekaru takwas sannan daga bisani a matsayin kwamishinan kananan hukumomi da harkokin masarautu kuma wannan nadin a wajena don ci gaba daga inda na tsaya ne wajen yi wa al'ummata hidima don kawo sauyi na ci gaba."

Gwamnan Gombe ya rantsar da Njodi a matsayin sakataren gwamnatin jihar

A wani labarin kuma, gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya rantsar da Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi a matsayin sakataren gwamnatin jihar (SSG) a ranar Litinin, 17 ga watan Yuli.

A kwanan nan ne gwamnan ya sake nada Ndoji a matsayin SSG bayan ya rike mukamin a gwamnatinsa na farko tsakanin 2019 da 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng