Shugaba Tinubu Ya Aike da Sakon Ta'aziyya Ga Dahiru Mangal da Imam Adigun

Shugaba Tinubu Ya Aike da Sakon Ta'aziyya Ga Dahiru Mangal da Imam Adigun

  • Shugaban ƙasa Tinubu ya yi ta'aziyya ga fitaccen attajirin ɗan kasuwar nan, Alhaji Dahiru Mangal bisa rasuwar matarsa
  • Haka nan Tinubu ya jajanta wa babban Malamin addinin Musulunci, Imam Adigun bisa rasuwar mahaifiyarsa ranar Laraba
  • Shugaban ƙasar ya yi Addu'ar Allah ya sa Aljannatul Furdausi ta zama makomar mamatan, Ameen

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya aike da saƙon ta'aziyya ga shugaban kamfanin sufurin jiragen sama Max Air da kamfanin AFDIN Group, Alhaji Dahiru Barau Mangal.

Tinubu ya yi ta'aziyya ga fitaccen ɗan kasuwan ne bisa rasuwar matarsa, Hajiya Aisha, wacce Allah ya yi wa rasuwa a karshen makon da ya gabata, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Shugaba Tinubu Ya Aike da Sakon Ta'aziyya Ga Dahiru Mangal da Imam Adigun Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

A kalaman da shugaba Tinubu ya aike wa Mangal, attajirin ɗan kasuwa ɗan asalin jihar Katsina, ya ce ya shiga damuwa yayin da ya samu labarin rasuwar matarsa.

Kara karanta wannan

APC Ta Tabbatar da Cewa Shugaba da Sakataren Jam'iyya Sun Yi Murabus, Ta Maye Gurbinsu

Tinubu ya jajanta wa Imam Adigun

Haka nan kuma shugaban ƙasa ya yi ta'aziyya ga shugaban majalisar malamai da limaman birnin tarayya Abuja kuma babban limamin masallacin Fouad Lababidi Central Mosque, Wuse, Dakta Tajudeen Adigun.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Leadership ta ce Tinubu ya jajanta wa Fitaccen Malamin Musuluncin ne bisa rasuwar mahaifiyarsa, Hajiya Aishatu Muhammad Adigun.

Marigayya Hajiya Aishatu ta rasu ranar Laraba kuma an yi mata Jana'iza kamar yadda Addinin Musulunci ya tanada washe gari ranar Alhamis a Offa, jihar Kwara.

Shugaba Tinubu ya buƙaci Malamin ya ƙara hakuri kuma ya kwantar da hankali duba da kyawawan ɗabi'u da ayyuka nagari da aka shaidi mahaifiyarsa kafin ta rasu.

A sanarwan ta'aziyya da kakakin shugaban ƙasa, Dele Alake ya fitra ranar Litinin, Tinubu ya yi Addu'ar Allah ya sanya mamatan a cikin gidan Aljannatul Firdausi.

Kara karanta wannan

Bayan Gana Wa da Tinubu a Villa, Babban Sarki Mai Martaba Ya Aike da Sako Mai Jan Hankali Ga Yan Najeriya

Buhari ya yi ta'aziyya ga Imam Adigun

Tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya jajanta wa Imam Adigun bisa wannan babban rashi da ya yi. Ya yi Addu'ar Allah ya mata rahama.

Saƙon ta'aziyyar Buhari ga fitaccen jagoran Musulmai, wanda yanzu haka yana ƙasa mai tsarki inda yaje aikin hajji, na kunshe a wata sanarwa da Malam Garba Shehu ya fitar.

Gwamnonin Kudu da Shugabannin Igbo Zasu Gana da Tinubu Kan Muhimmin Abu 1

A wani rahoton kuma Gwamnonin shiyyar Kudu maso Gabas da shugabannin Inyamurai zasu gana da shugaba Tinubu kan matsalar da ta addabe su.

Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo ne ya bayyana haka jim kaɗan bayan neman izini daga Tinubu a Aso Villa, Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262