Hukumar 'Yan Sandan Najeriya Ta Karyata Sanarwar Janye Jami'anta Daga 'Yan siyasa
- Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce labarin janye jami'an tsaro daga 'yan siyasa da aka ce ta yi ba gaskiya ba ne
- Rundunar ta kuma ce takardar da aka yaɗa musamman a kafafen sada zumunta ta bogi ce ba ta gaskiya ba
- Hukumar ta kuma yi kira ga 'yan Najeriya da su kasance masu lura sosai wajen tantance labaran gaskiya da na bogi
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta musanta labarin da ake yaɗawa na cewa ta janye jami'anta dake bai wa ‘yan siyasa kariya.
Jami'in hulɗa da jama'a na 'yan sandan Najeriya, CSP Olumuyiwa Adejobi ne ya bayyana hakan ta shafin rundunar na Tuwita.
'Yan sanda sun ce takardar ta bogi ce
Ya ce takardar wacce aka yaɗa mai ɗauke da umarnin cewa an janye jami'an ‘yan sanda daga wasu manyan ‘yan siyasa da ‘yan uwansu ta bogi ce.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya ƙara da cewa, takarda ta saɓa da ƙa'idar yadda suke fitar da saƙonninsu domin kuwa tana ɗauke da sanya hannun da ba shi ne ya dace ba.
Da yake mayar da martani kan batun, Sufeto-Janar na ‘yan sandan Najeriya, IGP Kayode Adeolu Egbetokun, PhD, NPM, ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan inda aka samu takardar ta bogi.
An shawarci 'yan Najeriya su riƙa tantance labaran da suke yaɗawa
Egbetokun ya kuma ba da tabbacin cewa, za a ɗauki matakin da ya dace a kan waɗanda suka ƙirƙiro ƙaryar da kuma yaɗa ta.
Wannan bayanin dai zai kwantar da hankalin 'yan siyasa da 'yan uwansu da suka ɗaga hankalinsu dangane da labarin ƙaryar da aka yaɗa kamar yadda Nigerian Tribune ta wallafa.
Rundunar 'yan sandan ta kirayi 'yan Najeriya da su riƙa sanya idanu sosai wajen tantance labaran gaskiya da na ƙarya, musamman ma wanda ake ɗorawa a a kafafen sada zumunta.
'Yan sanda sun kama masu garkuwa da mutane bakwai a Bauchi
Legit.ng a baya ta kawo muku rahoto cewa , jami'an hukumar 'yan sanda reshen jihar Bauchi, sun yi nasarar cafke wasu mutane bakwai da ake zarginsu da garkuwa da mutane.
An bayyana cewa an kama mutanen ne a yankin alƙaleri da ke jihar.
Asali: Legit.ng