Tashin Hankali: Yan Bindiga Sun Halaka Mutum 6 a Kauyukan Jihar Benuwai
- 'Yan bindiga sun aikata mummunan ta'adi a garuruwa biyu ranar Lahadi da daddare a jihar Benuwai
- Rahoto ya nuna maharan sun halaka rayukan mutum 6 yayin da suka kai farmaki kauyukan da ke ƙaramar hukumar Ushongo
- Mai magana da yawun jam'iyyar PDP, Bemgba Iortyom, wanda ya fito daga yankin ya tabbatar da faruwar lamarin
Benue - Miyagun 'yan bindigan da ba'a san ko su waye ba sun kai kazamin farmaki kauyukan Igba-Ukyor da kuma Tse Baka da ke ƙaramar hukumar Ushongo a jihar Benuwai.
Jaridar Punch ta tattaro cewa a harin na ranar Lahadi, 16 ga watan Yuli, maharan sun halaka rayukan mutum shida a ƙauyukan guda biyu.
A cewar wani mazaunin yankin, yan bindigan sun shiga garin Igba Ukyor a kan Babura kuma daga zuwa suka bude wa mutane wuta kan mai uwa da wabi, suka kashe mutane 5.
Farin Ciki: Sojoji Sun Kama Wasu 'Yan Kasar Waje Da Ke Kokarin Shigo Da Muggan Makamai Cikin Najeriya Maƙare A Mota
Mutumin, wanda ya nemi a sakaya bayanansa, ya ce bayan nan maharan sun shiga ƙauyen da ke maƙotaka da nan, inda suka kashe mutum ɗaya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Jaridar Tribune Online ta rahoto shi yana cewa:
"Sakamakon farmakin 'yan bindiga, mutanen kauye da yawa sun gudu zuwa cikin daji jiya da daddare saboda tsoron abinda ka iya faruwa, sai da safe suka dawo."
Jam'iyyar PDP ta tabbatar da faruwar lamarin
Kakakin PDP na jihar, Bemgba Iortyom, wanda ya fito daga ƙaramar hukumar da abun ya faru, ya tabbatar da cewa mutane 6 ne suka mutu a lokacin harin.
A kalamansa ya ce:
"Bayanan da na tattara sun nuna cewa yan bindiga a kan baburan Bajej sun kai hari Igba-Ukyor da misalin ƙarfe 8:00 na daren jiya (Lahadi) suka buɗe wuta, take mutum 5 suka ce ga garinku nan."
"Daga nan suka wuce kauyen Tse Baka da ke kusa da nan, suka yi ajalin wani mutum ɗaya. Har yanzun ban samu asalin sunayensu ba."
Rahoto bai riske mu ba har yanzu - Hukumar 'yan sanda
Jami'ar hulɗa da jama'a ta rundunar yan sandan jihar Benuwai, SP Catherine Anene, ta shaida wa manema labarai cewa har yanzu rahoto bai iso gare ta ba.
Talauci da Jahilci Ne Suka Haddasa Ayyukan Yan Bindiga a Arewa, Sani Yerima
A wani labarin na daban kuma Tsohon gwamnan Zamfara ya bayyana muhimman abu 2 da suka haifar da 'yan bindigan daji a arewacin Najeriya.
Sanata Ahmed Sani Yerima ya ce idan ka kalli duk masu hannu a lamarin, zaka ga talauci da jahilci ne suka jefa su ciki.
Asali: Legit.ng