Jerin Takwarorin Shugaba Tinubu Gwamnonin 1999 Da Aka Taba Garkame Wa
A ranar Laraba, 12 ga watan Yuli, Shugaba Bola Tinubu ya gana da takwarorinsa gwamnoni na shekarar 1999 a fadar shugaban ƙasa da ke birnin tarayya Abuja.
Tawagar tsaffin gwamnonin dai su ne na farko da aka fara zaɓa tun bayan dawowar mulkin dimokuraɗiyya a shekarar 1999, bayan an kwashe shekara 16 ana mulkin soja.
Shugaba Bola Tinubu yana daga cikin ƴan siyasar da aka zaɓa a matsayin gwamna a shekarar ta 1999. Shekara 20 bayan zaɓensu, abubuwa da dama sun faru da su ciki har da waɗanda aka garkame a gidan gyaran hali.
Ga jerin waɗanda suka taɓa yin zaman gidan kaso daga cikinsu wanda Legit.ng ta tattaro:
James Ibori
Ibori shi ne zaɓaɓɓen gwamnan jihar Delta daga shekarar 1999 zuwa 2007.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
An cafke shi inda aka tuhume shi da laifukan cin hanci kusan 170, amma wata babbar kotu a birnin Asaba ta wanke shi a shekarar 2009.
Kotun Southwark Crown a UK ta ɗaure tsohon gwamnan har na shekara 13 a gidan kaso bisa safarar haramtattun kuɗaɗe. Bayan shekara huɗu a gidan kaso, an sake shi bayan umarnin kotu a shekarar 2016.
Jolly Nyame
An zaɓe shi a matsayin gwamnan jihar Taraba a shekarar 1999 inda ya yi mulkin jihar har sau biyu wanda ya ƙare a shekarar 2007.
Hukumar EFCC ta cafke Jolly Nyame kan zargin cin hanci na N1.64bn. An yanke masa hukuncin shekara 12 a gidan kaso a shekarar 2018.
Joshua Dariye
Dariye an zaɓe shi a matsayin gwamnan jihar Plateau a shekarar 1999 a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), amma an tsige shi shekara uku bayan ya koma mulkin jihar a karo na biyu.
Shugaba Tinubu Har Yanzu Bai Tare a Gidansa na Villa Ba, An Bayyana Muhimmin Dalilin Da Ya Janyo Hakan
Hukumar EFCC ta tuhumi Dariye da zarge-zarge 23 kan safarar kuɗin haram, a ranar 12 ga watan Yulin 2018, an yanke masa hukuncin shekara 10 a gidan kaso.
Tinubu Ya Gana Da Takwarorinsa Gwamnonin 1999
Rahoto ya zo cewa Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gana da tawagar gwammnonin da aka zaɓa a shekarar 1999.
Shugaba Tinubu wanda yana daga cikin gwamnonin da aka zaɓa a shekarar 1999 ya gana da takwarorin nasa ne a birnin tarayya Abuja.
Asali: Legit.ng