Darajar Naira Ta Yi Kasa Yayin Da Hauhawar Farashi Ya Koma Kaso 22.7%, Na 11 Mafi Muni a Afirika
- Hauhawar farashi a Najeriya ya sake tashin gwauron zaɓi a watan Yuni, wanda hakan ya ƙara jefa ƴan Najeriya cikin talauci
- Ƙiddigar wacce hukumar NBS ta fitar, ta nuna cewa ƴan Najeriya na kashe kuɗi sosai wajen siyan abinci, kayayyaki da sauran kayan amfani a gida
- Yanzu da hauhawar farashin ya kai kaso 22.7%, Najeriya ta zama ta 11 a cikin jerin ƙasashen Afirika da hauhawar farashi ya yi ƙamari
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Hukumar ƙididdiga ta ƙasa (NBS) ta bayyana cewa hauhawar farashi ya tashin gwauron zaɓi a watan Yuni inda ya koma kaso 22.79% a watan Yunin 2023 saɓanin kaso 22.41% da yake a watan Mayu.
Hukumar NPS ta bayyana hakan ne a cikin sabon rahoton CPI da ta fitar a ranar Litinin, 17 ga watan Yulin 2023 wanda Legit.ng ta samu.
Yadda hauhawar farashin watan Yuni ya ƙaru
A cewar rahoton na NBS, hauhawar farashin na watan Yuni ya ƙaru da 0.38% idan aka haɗa da hauhawar farashin watan Mayu.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Hukumar ta kuma ce hauhawar farashin ya ƙaru a rahoton shekara-shekara da kaso 4.19 idan aka kwatanta da na watan Yunin 2022, wanda yake a kaso 18.60%.
Hauhawar farashin kayan abinci
Rahoton na NBS ga kuma bayyana cewa hauhawar farashin kayan abinci ya sake ƙaruwa a watan Yuni zuwa kaso 25.25% sabanin kaso 24.82% da yake a watan Mayu.
Ƙarin hauhawar farashin kayan abincin a shekara-shekara ya ƙaru ne saboda ƙarin kuɗin mai, buredi, madara, kifi, kayan itatuwa, nama, doya, ƙwayaye da sauransu.
Matsayin Najeriya a cikin ƙasashe masu hauhawar farashi
Wannan sabon hauhawar farashin ya nuna cewa yanzu Najeriya tana da matsayi na 12 a cikin jerin ƙasashen Afirika masu hauhawar farashi mafi muni a cewar bayanan Trading Economics.
Peter Obi Ya Yi Magana Kan Tallafin N8,000 Na Shugaba Tinubu, Ya Gayawa 'Yan Najeriya Muhimmin Abu 1 Da Za Su Yi
Ga jerin ƙasashen da su ke da hauhwar farashi mafi muni a Afirika
- Nigeria: 22.79%
- Sao Tome and Principe: 23.2%
- Congo: 26.67%
- Burundi: 28.9%
- Malawi: 29.2%
- Ethiopia: 29.3%
- Egypt: 35.7%
- Ghana: 42.5%
- Sierra Leone: 44.43%
- Sudan: 63.3%
- Zimbabwe: 176%
Abubuwan Sani Dangane Da Hauhawar Farashin Kaya
A baya rahoto ya zo kan muhimman abubuwan sani dangaane da hauhawar farashin kayayyaki da yake ƙara ƙamari.
A rahoton an yi duba kan abubuwa takwas waɗanda ke haddasa hauhawar farashin kayayyaki.
Asali: Legit.ng