Babu Inda Aka Nuna Wa Musulmai Wariya A Mukaman Gwamnatin Adeleke, Kungiyar Musulmi Ta Yi Karin Haske

Babu Inda Aka Nuna Wa Musulmai Wariya A Mukaman Gwamnatin Adeleke, Kungiyar Musulmi Ta Yi Karin Haske

  • Kungiyar Musulmai a jihar Osun (OSMC) ta ce babu inda gwamnan jihar, Ademola Adeleke ya nuna bambanci a nade-naden da ya yi a gwamnatinsa
  • Shugaban kungiyar, Sheikh Mustapha Olayiwola shi ya bayyana haka ga ‘yan jaridu inda ya ce a nade-naden da gwamnan ya yi akwai adalci a ciki
  • Ya ce gwamnan ya yi nade-naden mukamai manya-manya kuma na kusa da shi da suka hada da sakataren gwamnatin jihar da shugaban ma'aikata

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Osun – Kungiyar Musulmai ta Jihar Osun (OSMC) ta karyata jita-jitar cewa gwamnan jihar, Ademola Adeleke ya nuna wariya a jerin sunayen kwamishinoni.

Shugaban kungiyar, Sheikh Mustapha Olayiwola shi ya bayyana haka ga ‘yan jaridu inda ya ce gwamnan ya yi adalci a mukaman da ya nada a yanzu, cewar Leadership.

Babu Nuna Wariya Ga Musulmai A Mukaman Gwamnatin Osun, Kungiyar Musulmi
Ana Zargin Gwamna Ademola Adeleke Da Nuna Wariya A Sabbin Mukamai Da Ya Yi A Jihar. Hoto: BBC.
Asali: Facebook

Ana zargin gwamna Ademola Adeleke da nuna wariya a jerin sunayen kwamishinoni inda ya tura sunayen Kiristoci 17 yayin da Musulmai kuma bakwai, Vanguard ta tattaro.

Kara karanta wannan

Tarihi: Jerin gwamnoni 6 da suka taba yin mataimakin gwamna a jihohinsu

Kungiyar ta ce gwamnan ya nada Musulmai da dama a gwamnatinsa

A cewar shugaban kungiyar:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Gwamnan ya nada wasu mukamai na kusa da shi wadanda dukkansu Musulmai ne.
“Shugaban ma’aikata da sakataren gwamnatin jihar da masu ba shi shawara da sauran manyan mukamai duka Musulmai ne.
“Bayan haka, nadin kwamishinoni a jihar wannan ba hujja ba ne saboda akwai abubuwa da dama da ake dubawa.”

Ya shawarci Musulmai da su tsunduma harkar siyasa

Ya kara da cewa:

“A yanzu mun amince da dukkan nade-naden da ya yi kuma babu wani nuna wariya a Musulmai a jihar.
"Nadin mukamai da dama na zuwa kuma Musulmai da dama za su samu shiga.
“Shawarar da za mu bayar shi ne ya kamata Musulmai su shiga siyasa a dama da su madadin su tsaya a gefe suna cewa siyasa ba ta mutanen kirki ba ce.”

Kara karanta wannan

Shugaban kasa Tinubu Ya Baiwa Gbajabiamila Da Wasu Sabbin Mukamai

Kungiyar MURIC ta soki gwamnan da nuna wariya da yi wa kungiyar CAN aiki wurin nadin kwamishinoni a jihar, inda ake zargin ya fitar da sunayen Kiristoci 17 yayin da na Musulmai kuma bakwai.

MURIC Ta Zargi Gwamna Adeleke Na Jihar Osun Da Nuna Wariya Ga Musulmai

A wani labarin, kungiyar kare hakkin Musulmai (MURIC) ta soki gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke kan nuna wariya ga Musulmai.

Kungiyar na zargin gwamnan da yi wa Kungiyar CAN aiki a mukaman da ya nada a kwanan nan.

Ana zargin Adeleke ya tura sunayen kwamishinoni 17 Kiristoci yayin da aka samu sunayen Musulmai bakwai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.