Majalisar Wakilai Za Ta Tantance Sabbin Hafsoshin Tsaro a Ranar Litinin, 17 Ga Watan Yuli
- Majalisar wakilai ta shirya tantance manyan sabbin hafsoshin tsaro da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa
- Rahotanni sun tabbatar da cewa da hafsoshin tsaron za su bayyana a gaban majalisar wakilan a ranar Litinin, 17 ga watan Yuli
- Hakan na zuwa ne bayan majalisar dattawa ta tantance hafsoshin tsaron inda ta amince da naɗin da Shugaba Tinubu ya yi musu
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT, Abuja - Sabbin manyan hafsoshin tsaron da Shugaba Tinubu ya naɗa, za a ƙara tantance su a majalisar wakilai biyo bayan tantancewar da aka yi musu a majalisar dattawa satin da ya gabata.
A cewar rahoton Channels TV online, hafsoshin tsaron za su bayyana a gaban ƴan majalisar wakilan domin tantance su a ranar Litinin, 17 ga watan Yuli.
An tabbatar cewa tantance hafsoshin tsaron za a gudanar da shi ne a keɓe a majalisar wakilan, rahoton The Nation ya tabbatar.
Hafsoshin tsaron da Shugaba Tinubu ya naɗa su ne he Manjo Janar Christopher Musa (babban hafsan tsaro na ƙasa), Manjo Janar Taoreed Lagbaja (shugaban hukumar sojin ƙasa), Rear Admiral Emmanuel Ogalla (shugaban hukumar sojin ruwa), da AVM Hassan Abubakar (shugaban hukumar sojin sama).
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majalisar dattawa ta tantance hafsoshin tsaro
A lokacin da majalisar dattawan ta tantance hafsoshin tsaron a satin da ya gabata, shugaban majalisar dattawan, Godswill Akpabio, ya ce hafsoshin tsaron sun amsa tambayoyi kan batutuwan da suka shafi tsaro da sauran batutuwa.
A wata wasiƙa da aka karanta a majalisar a ranar Litinin, 10 ga watan Yuli, shugaban ƙasa Tinubu ya buƙaci majalisar dattawan da ta amince da naɗin hafsoshin tsaron.
Bayan majalisar ta dawo zamanta a ranar Alhamis, 13 ga watan Yuli, majalisar ta fara tantance hafsoshin tsaron, inda kowannensu ya hau kan dandamalin majalisar ya yi magana kan yadda zai magance matsalar tsaro a ƙasar nan idan aka amince da naɗinsa.
Nadin Hafsoshin Tsaro Ya Samu Amincewar Majalisa
A wani labarin kuma, majalisae dattawan Najeriya ta amince da naɗin sabbin hafsoshin tsaron ƙasa da Shugaba Tinubu ya yi.
Majalisar dattawan ta amince da naɗin na su ne biyo bayan kammala tantancewar da ta yi musu.
Asali: Legit.ng