Shugaba Tinubu Har Yanzu Bai Tare a Gidansa na Villa Ba, An Bayyana Dalilin Hakan

Shugaba Tinubu Har Yanzu Bai Tare a Gidansa na Villa Ba, An Bayyana Dalilin Hakan

  • Har yanzu Shugaba Tinubu bai tare a gidansa na fadar shugaban ƙasa ba duk da cewa ya kwashe sati shida akan karagar mulki
  • Tsaikon da aka samu ya faru ne a dalilin aikin gyare-gyaren da aka fara a lokacin da tsohon Shugaba Buhari ya bar gidan
  • Gyaran da ake yi ya ƙunshi sake fenti da sanya sabbin kayan ɗaki, sannan za a bar zaɓi ga Tinubu kan irin kayan da yake so a sanya masa a gidan

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Duk da ya kwashe sati shida akan karagar mulki, Shugaba Bola Tinubu har yanzu bai koma gidansa ba a cikin fadar shugaban ƙasa ta Aso Rock Villa, a birnin tarayya Abuja.

A yayin da yake amfani da ɗakin taronsa na musamman, ofishinsa domin gudanar da tarurruka masu muhimmanci da baƙi na gida da waje, har yanzu bai tare a gidansa ba, The Punch ta rahoto a ranar Lahadi, 16 ga watan Yuli.

Kara karanta wannan

Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai Ya Bayyana Yadda Wani Yankin Najeriya Ya Yi Asarar N4trn Cikin Shekara Biyu Saboda Dalili 1 Rak

Har yanzu Shugaba Tinubu bai tare a Villa ba
Gyaran da ake yi ya hana Shugaba Tinubu ya tare a Villa Hoto: @DOlusegun
Asali: Facebook

Dalilin da yasa bai tare a gidansa na Villa ba

Dalilin samun wannan tsaikon a cewar jaridar The Punch, ka iya yiwuwa saboda aikin gyaran da ake yi wanda aka fara lokacin da tsohon Shugaba Buhari ya fice daga gidan ya koma wani gida na wucin gadi da ake kira da 'Glass House'.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Legit.ng ta tattaro cewa an fara yin garambawul a fadar shugaban ƙasa a ranar 6 ga watan Mayun 2023, ƴan kwanaki kaɗan kafin a rantsar da Shugaba Tinubu.

Gyare-gyaren da ake yi sun haɗa da yin sabon fenti ga wuraren da suka ƙoƙe da sauya sabbin kujeru da kayan ɗaki da sauran abubuwa daban.

Wata majiya a cewar jaridar ya yi nuni da cewa, Shugaba Tinubu kamar magabatansa zai faɗi irin kayan da yake so a sanya masa a gidan.

Kara karanta wannan

Badakalar N1bn: Kotu Ta Bayar Da Sabon Umarni a Shari'ar Tsohon Kwamishinan Ganduje

"Tinubu bai tare ba saboda aikin gyare-gyaren da ake ta yi yanzu haka." A cewar wata majiyar.

Kwamitin Rabon Kayan Tallafi Ya Fitar Da Sabbin Bayani

A wani labarin kuma, kwamitin rabon kayan tallafi na Shugaba Tinubu domin rahe raɗaɗin cire tallafin man fetur ya fitar da sabbin bayanai.

Shugaban kwamitin kuma gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, ya bayyana cewa nan bada daɗewa ba ƴan Najeriya za su dara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng