Jama’a Sun Girgiza Bayan da Budurwa Ta Nuna Ruwa a Doguwar Leda da Ta Siya N10 Kacal a Benin
- Wata kyakkyawar ‘yar Najeriya ta jawo cece-kuce a shafin yanar gizo yayin da ta nuna ruwan ledan da ta siya N10 a Benin
- Da take yada bidiyon, ta caccaki masu siyar da ruwan ledar da aka fi sani da ‘pure water’ da ‘yan handama
- ‘Yan Najeriya da sauran mutane a kafar sada zumunta sun bayyana ra’ayoyinsu bayan ganin abin da ya faru
Wata ‘yar Najeriya mai suna Ronke Mopheth ta yadu a kafar sada zumunta yayin da ta nuna irin ruwan ledar da ta siya a jihar Edo a kan kudi N10.
A bidiyon, an ga lokacin da budurwar ke rike da ledar cikin farin ciki, inda take bayyana arahar kayayyaki a jihar ta Edo.
Yayin nuna ruwan a doguwar leda, ta ce N10 kacal ta siya a lokacin da ta ziyarci kakarta a wani yankin jihar.
Ta alakanta yadda farashin ruwan leda yake a birnin Benin da kuma yadda farashin yake a birnin Legas, inda ake siyar da ruwan leda N50.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Kalli bidiyon:
Martanin jama’a a kafar sada zumunta
Batun nata dai ya jawo cece-kuce da martani a kafar sada zumunta, inda wasu zargin ruwan bai da tsafta ma kwata-kwata. Wasu kuwa na cewa, watakila ma ruwan rafi ne. Ga dai abin da ake cewa:
topmost_02:
“’Yar uwa gwamma ki gudu kada ki sayi typhoid ki sha ki zaci abu ne mai kyau. Farashin a hankalce ba zai yiwu ba ace mutum ya sha ruwan ba.”
fekomi:
“Kawai kin sha spirogyra bayan kin sha ruwan N10 za ki zo ki kashe 2M na zuwa asibiti kuwa.”
officialmikemore:
“Baki ma ko tsoro. Kika saya kuma sha. Ya miki kyau.”
achiles30ers:
“A zagaye yake da typhoid da sauran cukuta 20.”
mrkaylem:
“’Yar uwa yadda kaya yake da tsada a kasuwa amma mutum ya baki ruwan nan N10 kuma ki karba ba tsoro?”
Yadda wata budurwar ta fasa asusunta ya ba da mamaki
A wani labarin, wata baiwar Allah ta cika da farin ciki yayin da ta fasa dan akwatin da ta yi asusun kudade bayan ta kwashe watanni tana ajiya.
Wani faifan bidiyo mai daukar hankali da aka yada a TikTok, ya dauki lokacin da ta fasa asusun don bayyana makudan kudin da ta tara.
Ta yi kururuwa a cikin faifan bidiyon don nuna mamakinta da murna kan yadda ta tara kudade masu yawa a cikin wasu ‘yan watanni.
Asali: Legit.ng