Jama’a Sun Girgiza, Sun Yi Martani Bayan Ganin Yadda Wata Mata Ta Tara Kudade Masu Yawa a Asusu

Jama’a Sun Girgiza, Sun Yi Martani Bayan Ganin Yadda Wata Mata Ta Tara Kudade Masu Yawa a Asusu

  • Wata budurwa ta yanke shawarar cewa lokaci ya yi da za ta fasa asusunta bayan watanni da ta yi tana ajiye kudi a ciki
  • A cikin faifan bidiyo da aka yada a TikTok, ta fito da guduma wanda ta yi amfani da shi don fasa asusun nata
  • Adadin kudaden da suka fito yayin da ta fasa asusun ya ba mutane da yawa mamaki, inda wasu suka shajja’a da fara tarun kudi

Wata baiwar Allah ta cika da farin ciki yayin da ta fasa dan akwatin da ta yi asusun kudade bayan ta kwashe watanni tana ajiya.

Wani faifan bidiyo mai daukar hankali da aka yada a TikTok, ya dauki lokacin da ta fasa asusun don bayyana makudan kudin da ta tara.

Ta yi kururuwa a cikin faifan bidiyon don nuna mamakinta da murna kan yadda ta tara kudade masu yawa a cikin wasu ‘yan watanni.

Kara karanta wannan

Ka ji tausayi: Yadda fasto ya tara dandazon jama'a suka yi girki a sansanin gudun hijira

Budurwa ta tara kudin da ba a yi tsammani ba
Kudaden da wata budurwa ta tara a kasar waje | Hoto: @its_vivianette/TikTok, Westend61/ Getty Images
Asali: UGC

Kalli bidiyon:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Martanin jama’a yayin da matar ta fasa asusunta

Masu amfani da shafin TikTok sun yi martani mai daukar hankali bayan ganin abinda ya faru da matar, inda suka shajja’a da sha’awar tara kudi kamar yadda ta yi. Ga kadan daga abin da suke cewa:

@sunnynfxpcr:

“Wannan da nine da ace bani da ‘yan uwa.”

@tifahivy7:

“Ni kenan, ba dan ina son kashewa kaina kudi ba.”

@tara3546:

“Da ni ne a banki zan saka su na ci gaba da ajiye wa a asusun ajiya.”

@stitchisthecutess:

“Ku mayar dashi Amazon idan da ace ni da Amazon babu mu, ku ambace ni”

@rumbivpq2m2:

“Ni kenan idan KFC da Roman’s Pizza suka rufe har abada kenan.”

@eduardo_espinal:

“Ni kenan idan na kammala biyan rancen dalibai da ake bi na na zango uku.”

Kara karanta wannan

Cikin minti 2: Matar aure ta koka kan yadda maza ke dirka wa mata ciki a kankanin lokaci

@diannexxl:

“Ni babu ruwa na da asusu. Ko don na fi kaunar mai yawa ne.”

@_anonymous721:

“Ni kenan idan aka ce kantuna basu da man gashi.”

Mata ta gina gidaje 2 mijinta bai sani ba

A wani labarin, kunji yadda wata mata ta gina gidaje guda biyu ba tare da sanin mijinta ba, ya yi kokarin daukar mataki.

A lokacin da ya tambaye ta dalilin boye masa, sai kawai ta kafta masa mari don nuna matsanancin fushinta.

A rahoton, mijin ya bayyana gaskiyar abin da ya faru da kuma yadda suka samu sabani tun farkon lamarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.