Dakarun Sojoji Sun Halaka 'Yan Ta'addan ISWAP Masu Yawa a Jihar Borno
- Dakarun sojoji sun yi ɓarin wuta kan ƴan ta'addan ƙungiyar ISWAP wacce ke gudanar da ayyukan ta'addanci a jihar Borno
- Dakarun sojojin dai su yi ɓarin wutar ne ta hanyar amfani da jiragen yaƙi kan maɓoyar ƴan ta'addan a yankin tafkin Chadi
- Sojojin sun yi nasarar lalata kayayyakin ƴan ta'addan da halaka da dama daga cikinsu bayan sun yi musu ruwan bama-bamai
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Borno - Dakarun sojojin Najeriya sun lalata maɓoyar ƴan ta'addan ƙungiyar Islamic State of the West African Province(ISWAP) sannan suka halaka da dama daga cikin mayaƙanta a Marte cikin jihar Borno.
Dakarun sojojin sun samu wannan nasarar ne bayan hare-haren da suka kai ta jiragen sama a cikin ƴan kwanakin nan bayan sun samu bayanan sirri kan maɓoyar ƴan ta'addan.
Dakarun Sojoji Sun Yi Gumurzu Da 'Yan Bindiga Sun Ceto Mutane Masu Yawa Da Suka Sace a Arewacin Najeriya
Binciken da dakarun sojojin su ka yi ya nuna musu akwai gungun ƴan ta'adda a Kollaram da Arinna Ciki.
Dakarun sojojin sun yi wa ƴan ta'addan ruwan bama-bamai
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zagazola Makama, wani masani kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi ya samo daga majiyoyin sirri cewa jiragen yaƙin sojojin saman Najeriya biyu sun saki bama-bamai da yammacin ranar 15 ga watan Yuli a yankin Arinna Chiki na tafkin Chadi.
Majiyoyin sun ƙara da cewa wasu gungun ƴan ta'addan an sakar musu bama-bamai suna cikin kwale-kwale lokacin da su ke ƙoƙarin tsallaka tafkin su haɗu da takwarorinsu a Tumbun Rego domin kai wa jami'an tsaro hari.
Jirgin yaƙin wanda ya riƙa yin luguden wutar kan ƴan ta'addan ya lalata musu kayayyaki masu yawa tare da halaka ƴan ta'addan masu yawa a yayin harin.
A cikin ƴan kwanakin nan dai dakarun sojoji sun ƙara matsa ƙaimi wajen kai hare-hare kan ƴan ta'addan da suka daɗe suna addabar al'ummar jihar Borno.
Dakarun Sojoji Sun Halaka Mayakan ISWAP
A wani labarin kuma, dakarun sojojin saman Najeriya sun aike da mayakan ƙungiyar ISWAP zuwa inda ba a dawowa.
Dakarun sojojin sun halaka mayakan ƙungiyar da dama a wani luguden wuta da suka yi musu a jihar Borno.
Asali: Legit.ng